HUKUNCIN AIKI A HOTEL DIN DA AKE SIYAR DA GIYA


HUKUNCIN AIKI A HOTEL DIN DA AKE SIYAR DA GIYA

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum ya Sheikh inada tambaya
Hukuncin yin aiki a matsayin accountant ko receptionist a hotel da suke da sashin sayar da giya aciki.

*AMSA*👇

Wa'alaykumussalam
Baya halatta ayi aiki a irin wannan hotel din ba don daga cikin wadan da manzon Allah ya ce Allah ya la'ance su akwai "... Mai saida giya da mai cin kudin giya" kamar yadda ya tabbata cikin hadisin Abdullahi dan Umar da Anas dan Malik wanda Abu Dauda 3674, Ibn Maaja 3380, da Tirmizy 1295 Suka ruwaito.
Sannan kuma yin irin wannan aikin taimakawa ne wajen barna da baiwa mai barnar mafaka wanda shima manzon Allah yace Allah ya tsinewa mai ba mabarnaci mafaka a cikin hadisin Aliyu bn Abi-Dalib wanda Muslim ya ruwaito 1978.

Allah ya kara tsare mana su da mu baki daya.

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)