*Sallama Da Hukunce-Hukuncenta*
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
1) Sallama wata abace mai muhimmnci wanda Addininmu na Musulunci ya karantar damu a duk lokacin da muka hadu da daya daga cikinmu mu yi ta tare da yin musafaha (haɗa hannaye). Amma a yau mun wayi gari mukan fifita gaisuwa irin ta al'ada akan gaisuwar Musulunci. Tun daga kan manyanmu har k'ananunmu. Saboda haka yana da kyau mu rika tunasar da junanmu akan ta musamman ga dalibai a makarantu na Islamiyya da wasu wuraren karatuka.
2) Allah Ta'ala yana cewa: "Yaku da kuka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama ga masu gidan".
Suratu Núr, aya ta: 27.
Allah Ta'ala ya sa ke faɗi cewa: "Idan zaku shiga gida, to kuyi sallama a kan kawunanku, gaisuwa daga Allah mai albarka, dadádã". Surah: Nùr, 61.
Allah Ta'ala ya sake fadi: "Idan an gaishe ku da gaisuwa mai kyau to kuma ku gaishe su da wacce ta fita kyawu, ko kuma ku mayar da kwatankwacin wacce aka muku".
Surah: Nisa'i, aya ta: 86.
3) Abdullahi dan Salam radiyallahu anhu yace Manson Allah (S.A.W) yace: "Ya ku mutane ku yada sallama, ku sadar da zumunci, kuma kuyi salla da dare, lokacin da mutane ke bacci, sai ku shiga Aljanna tare cikin aminci". Tirmizi.
Abdullahi ɗan Amru radiyallahu anhu yana cewa: wani mutum ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) wani aiki ne mafi alkhairi? Sai Manson Allah (S.A.W) yace: Ciyarda abinci, sannan yin sallama ga wanda ka sa ni da wanda ba ka sa ni ba". Bukhari da Al-Imam Muslim.
Abu Hurairah radiyallahu anhu yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: " Ba zaku shiga Aljanna ba har sai kunyi imani, kuma ba zaku yi imani ba har sai kunso junanku, shin bana nuna muku abinda in kuka aikata shi zaku so juna ba? Ku yada sallama a tsakaninku". Al-Imam Muslim.
Imran dan Husain yace: wani mutum yazo wurin Manzon Allah (S.A.W) sai ya yi masa sallama "Assalamu alaikum" sai Manzon Allah (S.A.W) yace yana da lada goma, wani ga sake zuwa ya yi sallama da cewa: "Assalamu alaikum wa-rahmatullahi" sai Manzon Allah (S.A.W) yace yana da lada ashirin, sai ya sa ke zuwa shima ya yi sallama: "Assalamu alaikum wa-rahmatullahi wa-barakatuh" sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yace yana da lada talatin". Tirmizi.
4) Daga cikin hukunce-hukuncenta shine: Ya halasta maza suyiwa mata, haka suma mata suyiwa maza idan har an kubuta daga fitina, gabatar da ita akan gaisuwar al'ada, yin ta a duk lokacin da ka gamu da dan uwanka, ƙarami ya yiwa babba, jama'a kadan suyiwa masu yawa, nakan abin hawa ya yiwa na kasa, na tsaye ya yiwa na zaune.
5) Yana daga cikin tasirin da sallama ke da shi a cikin rayuwar musulmi: Aminci, samun yarda, sanya soyayya a tsakanin juna, hada zumunci. Allah Subhanahu Wata'ala ya bamu ikon yada sallama a tsakanin junanmu.