SHIN TSAKANIN ZAFI NA IYA SA A AJIYE AZUMI?


https://chat.whatsapp.com/D3VpiJzm6WECmizK6DEBfi
*SHIN TSANANIN ZAFI NA IYA SA A AJIYE AZUMI?*



*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum. Allah ya karawa rayuwar malam albarka. Tambaya ta itace: ya hallata al'umma su ajiye Azumi saboda tsananin zafi? Allah ya karawa rayuwar malam albarka. Daga Wa'alamu Gide Dan Ali

*AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Wannan fatawa na da hatsari don haka sai mai karatu ya bayar da kulawa da kyakkyawan nufi da zai haifar masa da kyakkyawan fahimta.

Amsa ita ce, eh, ya halatta mutum ya ajiye azumi, ya azumce shi a wani lokaci, saboda tsananin zafi, ba kowane irin zafi ba. Ƙa'ida ce, a wannan addini, tsanani na jawo sauƙi 

المشقة تجلب التيسير 

Allah ya faɗa cewa 

(إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَیۡكُمُ ٱلۡمَیۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِیرِ وَمَاۤ أُهِلَّ بِهِۦ لِغَیۡرِ ٱللَّهِۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَیۡرَ بَاغࣲ وَلَا عَادࣲ فَلَاۤ إِثۡمَ عَلَیۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمٌ)
[Surah Al-Baqarah 173]

Akwai labaru da ke iso mana cewa, a wasu garuruwa na ƙasar nan, mutane suna suma ko ɗora wa ƙanƙara ko suna kwarara ruwan sanyi a kan su, saboda tsananin zafi. Toh su sani babu tsanani a addinin mu 

(.. مَا یُرِیدُ ٱللَّهُ لِیَجۡعَلَ عَلَیۡكُم مِّنۡ حَرَجࣲ وَلَـٰكِن یُرِیدُ لِیُطَهِّرَكُمۡ وَلِیُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَیۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ)
[Surah Al-Ma'idah 6]

Toh a irin wannan yanayi, Allah shine shaida kuma shine masani na abin da ke ɓoye, sannan shine yace, baya kallafa wa rai sai abin da take da iko, don haka a duk lokacin da ya zamo mutum baya da ikon ɗaukar wani abin da Allah ya wajabta masa, shi ke nan, wannan umarni ya faɗi daga barin sa, Allah yace

(..... لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ.. )
[Surah Al-Baqarah 233]

Allah yace ka kaɗaita shi da bauta, amma bai ce ka kashe kan ka ba, ko ka raunata kan ka, shi yasa ya gina addinin a kan fandeshi da tubula na sauƙi, ya cire dukkan wani tsanani daga duk umarni da yayi mana, kuma ya ce sai muna iyawa, shi yasa zakka ta faɗi daga barin miskini, da faƙiri. Hajji yace ga mai iko. Sallah Annabi yace a tsaye za'a yi ta tilas, amma sai yace duk wanda bai iya tsayawa, yayi ta a zaune, wanda bai iya yin ta a zaune, yayi ta a kwance, wanda ko a kwance bai iyawa, shi ke nan ta faɗi daga kan sa.

Wallahu ta'aala a'lam.
Post a Comment (0)