WANE GROUP KAKE CIKI A SOCIAL MEDIA?



*WANE IRIN GROUPS KAKE CIKI A SOCIAL MEDIA?*
-
GABATARWA:
Hausa Islamic Pictures Quotes. 
-
πŸ‚Wasu sukan shiga groups na addinin musulunci domin su Ζ™aru su kuma faΙ—aku, suji wa'azi ko su karanta nasiha mai matuΖ™ar ratsa zuciya domin su Ζ™ara kusanci ga ubangijinsu Allah, wanda hakan kuma zai iya zame musu farin ciki a ranar lahira.
-
πŸ‚Wasu sukan shiga groups na siyasa ne domin su yabi wanda suke so ko kuma su caccaki abokin hamayyarsu, wanda hakan kuma zai iya zame musu nadama a ranar Ζ™iyamah.
-
πŸ‚Wasu sukan shiga groups Ι—in batsa ne domin su bawa idanunsu abinci ta hanyar kallon haramun, wanda hakan kuma zai iya zame musu asara da nadama a ranar lahira.
-
πŸ‚Wasu sukan shiga groups Ι—in fina-finai da comedies ne domin su sami nishaΙ—i da farin ciki, sun manta da cewa lallai babu wani alkhairi acikin duk wani jin daΙ—in da aka manta da Allah acikinsa.
-
"Dukkanin mu bayin Allah ne, kuma dukkanin mu masu yin kuskure ne, wanda yaji ko yaga kuskurensa kuma ya gyara shi, to haΖ™iΖ™a wannan shine yake da raubata, wanda kuma yaji ya gani ya sani sannan kuma ya wofuntar dashi, to lallai wannan sai yayi nadama a gaban Allah buwayi.
-
"Dukkanin wani groups Ι—in da kake cikinsu, matuΖ™ar kasan bazasu tunatar dakai lamarin Allah ba, to wallahi wannan mashiriricin group ne, kuma kayi gaggawar fita daga cikinsa kafin mutuwa ta riske ka, domin wallahi sai Allah yayi maka hisabi abisa duk irin groups ko pages Ι—in da kake cikinsu a social media, gyara ya rage naka a yanzu. 
-
Yaa Allah kasa mu zamto daga cikin datattun bayin ka waΙ—anda da zarar sunga kuskurensu suke Ζ™oΖ™arin gyarawa nan-take, Ameen.
-
✍🏿Hausa Islamic Pictures Quotes
Post a Comment (0)