WAI A CIKIN WATANNAN NA SHA'ABAN AKWAI WANI DARE LAILATUL BARA'A?



WAI A CIKIN WATANNAN NA SHA'ABAN AKWAI WANI DARE LAILATUL BARA'A?

https://chat.whatsapp.com/BLtOd0SfWGJ9MinvfShFw8

*TAMBAYA*❓

_Aslm Allah ya kara ma malan tsawaon rai amine Mal. tambaya ta shine wai acikin watannan akwai wani dare da ake kiransa da laylatul Bara`a mal. ina bukatan shari akan wannan dare_

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

_To bayin Allah idan na fahimceku kuna nufin daren Rabin sha'aban da wasu wadanda suka rafkana suke kebanceshi da wasu ibadu dasauransu shine wasu suke kira da lailatul bara'a. To a dunkule dai abinda ya tabbata shine: Babu wani nassi ingantacce daya kebance wani dare guda daya na watan sha'aban da wata falala ta musamman duk wani hadisi da kukaji ana bayyana falalar wani dare na watan sha'aban to be tabbata daga manzon Allah ﷺ ba kamar yadda malamai sukace._
.
_Zayd bin Aslam yace: Bamu taba ganin wani daga cikin malumanmu ko fuqaha suna cewa Laylat al'Baraa’ah (15 Sha’baan) yana da wani fifiko a kan sauran darare ba. Ibn Dihyah yace: Hadisai game da sallah a a Laylat al-Baraa’ah (15 sha'aban) 'kirkirarrune..... [ A Duba: *Tadhkirat al-Mawdoo'a'at na al-Fatni, shafi na.45]*_
..
_Imamu Al‘Iraaqi yace: Hadisinda yazo game da sallah a Laylat al-Nisf (tsakiyar Sha’baan) karya ne. Hakanan Ibn Al'Jawzi ya kawo hadisin a cikin al-Mawdoo'a'at (wato cikin jerin hadisai 'kir'kirarru wadanda aka 'kir'kira na 'karya). _Sabida haka hadisan basu tabbata ba._
.
_Imamun nawawi Allah yayi masa rahama ya faďa a cikin littafinsa *Almaj'mu* cewa: Sallar da akeyi ta tsakiyar watan sha'aban bidi'ace abar 'kyama._
..
Anyiwa Ibn Usaimin Allah yaji kansa da rahama tambaya game da kebance ranar 15 ga watan sha'aban na duk shekara da wasu nau'ikan ibadu. Sai ya bada amsa da cewa: *Ranar tsakiyar watan sha'aban bata da bambanci da sauran ranekun tsakiyar sauran watanni....* [Fataawa ibn usaimin 1/190]_
..
_Sabida haka a sunnah babu wani nassi ingantacce daya kebance wani dare daga cikin Dararen watan sha'aban da wata kebantacciyar falala. dareren watan sha'aban dadai suke dasauran dareren watanni, Amma dai babu laifi ga mutuminda da ya saba 'kiyamullaili ya tashi ya raya Dararen da ibadu ingantattu da suka tabbata a sunnah wannan kam babu laifi in sha Allahu, kamar yadda aka rawaito daga matan Manzon Allah ﷺ cewa: Manzon Allah ﷺ yana yawaita azumi a cikin wannan watan na sha'aban. Amma dai kebance wani dare na watan sha'aban ďin da wasu salloli na daban ko wasu nau'in ibadu bashi da asali a sunnah kamar yadda bayani ya gabata a can sama_
..
Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)