SALLAR YININ ALHAMIS BIDI'A CE TA ƳAN SHI'A



SALLAR YININ ALHAMIS BIDI'A CE TA ƳAN SHI'A

https://chat.whatsapp.com/BLtOd0SfWGJ9MinvfShFw8

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum warahmatullah,

Malam menene ingancin wannan hadisin
👇👇👇👇👇👇👇

Raka'ar farko: Fatiha 1, sai Qulhuwallahu 11
Raka'a ta biyu: Fatiha 1, Qulhuwallahu 21.
Sai a sallame, sai aci gaba:-
Raka'a ta Uku: Fatiha 1,Qulhuwallahu 31
Raka'a ta hudu: Fatiha 1, Qulhuwallahu 41
Idan an sallame, sai a karanta- Qulhuwallahu 51 a zauna, sannan a yi salatin Annabi (SAW), shima 51
Sai ayi sujjuda, a cikin sujjadar sai a ce; YAA ALLAHU" sau 100. Sai a roki Allah Ta'ala duk bukatar da ake so (acikin sujjadar)


 *AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.

Wannan sallah ce ta ƴan shi'a da suke kira da "sallar yinin Alhamis". Wannan na daga cikin Hadisai na ƙarya da maƙiyan Allah da Manzo, mabiya mazhabar shi'a suka ƙirƙira don ɓatar da bayin Allah da raba su da Sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam da musulunci, su kai su zuwa ga kafirci da jahilci da ta'addanci ga Allah da Manzo da Muminai, duk da sunan son Ali da Fatima, ko ahlul baiti, idan ka duba littafin su mai suna wasa'ilush shi'atu, mujalladi na huɗu, shafi na 32, sun jero waɗannan salloli tare da wasu addu'oi da Allah bai saukar da su ba, Manzo bai koyar ba, na yini da daren Alhamis daban daban. Wannan tana daya daga cikin su, ga ta nan yadda take rubuce a littafin su da yaren larabci, kafin wani ɓataccen ya ɗauki nauyin fassara ta zuwa yaren Hausa. 

 ﺻﻼﺓ ﺃﺧﺮﻯ ﻟﻠﺤﺎﺟﺔ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺨﻤﻴﺲ

ﻋَﻦِ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭﺁﻟﻪ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﺃَﻧَّﻪُ ﻗَﺎﻝَ ﻣَﻦْ ﺻَﻠَّﻰ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﺨَﻤِﻴﺲِ ﺃَﺭْﺑَﻊَ ﺭَﻛَﻌَﺎﺕٍ ﻳَﻘْﺮَﺃُ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄُﻭﻟَﻰ ﻣِﻨْﻬُﻦَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻋَﺸْﺮَﺓَ ﻣَﺮَّﺓً ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ﻭَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺜَّﺎﻧِﻴَﺔِ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻭَ ﻋِﺸْﺮِﻳﻦَ ﻣَﺮَّﺓً ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ﻭَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺜَّﺎﻟِﺜَﺔِ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻭَ ﺛَﻠَﺎﺛِﻴﻦَ ﻣَﺮَّﺓً ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ﻭَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﺍﺑِﻌَﺔِ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻭَ ﺃَﺭْﺑَﻌِﻴﻦَ ﻣَﺮَّﺓً ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ﻛُﻞَّ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺑِﺘَﺴْﻠِﻴﻢٍ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺳَﻠَّﻢَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﺍﺑِﻌَﺔِ ﻗَﺮَﺃَ ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻭَ ﺧَﻤْﺴِﻴﻦَ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَ ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻭَ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻭَ ﺧَﻤْﺴِﻴﻦَ ﻣَﺮَّﺓً ﺛُﻢَّ ﻳَﺴْﺠُﺪُ ﻭَ ﻳَﻘُﻮﻝُ ﻓِﻲ ﺳُﺠُﻮﺩِﻩِ ﻳَﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣِﺎﺋَﺔَ ﻣَﺮَّﺓٍ ﻭَ ﺗَﺪْﻋُﻮ ﺑِﻤَﺎ ﺷِﺌْﺖَ ﻭَ ﻗَﺎﻝَ ﺇِﻥَّ ﻣَﻦْ ﺻَﻠَّﻰ ﻫَﺬِﻩِ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَ ﻗَﺎﻝَ ﻫَﺬَﺍ ﺍﻟْﻘَﻮْﻝَ ﻟَﻮْ ﺳَﺄَﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻓِﻲ ﺯَﻭَﺍﻝِ ﺍﻟْﺠِﺒَﺎﻝِ ﻟَﺰَﺍﻟَﺖْ ﺃَﻭْ ﻓِﻲ ﻧُﺰُﻭﻝِ ﺍﻟْﻐَﻴْﺚِ ﻟَﻨَﺰَﻝَ ﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳُﺤْﺠَﺐُ ﻣَﺎ ﺑَﻴْﻨَﻪُ ﻭَ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺗَﻌَﺎﻟَﻰ ﻟَﻴَﻐْﻀَﺐُ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﻦْ ﺻَﻠَّﻰ ﻫَﺬِﻩِ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَ ﻟَﻢْ ﻳَﺴْﺄَﻝْ ﺣَﺎﺟَﺘَﻪُ .

Wannan hadisin ƙarya ne, baya cikin littafin Sunnah ko ɗaya, ka ƙalubalanci mutum yazo ma da ita a cikin littafin Sunnah ɗaya, babu, har ma hadisan ƙarya da Imamul Ghazzali ya tattaro cikin Ihya'u babu wannan.

Jama'ar musulmi maza da mata, yara da manya, na birni da na ƙauye, mu shiga taitayin mu, kuma mu yi hattara, shi'a tana yaɗuwa kamar wutar daji, sun shiga gwamnati kuma suna tsakankanin mu suna amfani da kuɗi da duk wata hanya, ko ka sani ko baka sani ba, kuma ko ka yarda ko kar ka yarda, haka abin yake, suna yaɗa mummunar aƙidar su da yi ma addinin su da mabiya su hidima da ƙoƙarin rusa ɗora mutane a kan ibadu na bogi da ɓatar da musulmi da rusa musulunci da tayar da fitina tsakanin al'umma. 

Maganin wannan masifa ko riga-kafin mu a yau shine, mu tashi mu nemi ilmi daga bakin Malamai na Sunnah ko mu tambaye su, mu yi aiki da abin da muka koya na ilmin, mu so junan mu, mu yaɗa aƙidar mu, mu zamo cikin shiri, kuma mu taimaki junan mu, wannan ita ce kaɗai hanyar tsira.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 _Malam Aliyu Abubakar Masanawa_ 

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)