WAI SHI’A MAZHABA CE
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA*❓
_Assalamu Alaikum._
Malam, wani saurayi ne muke aiki a wuri ɗaya da shi, shi ne na tambaye shi meyasa yake bin shi’a? Sai ya ce wai ai ita ma mazhaba ce, kamar dai sauran mazhabobi! Haka ne?
*AMSA*👇
_W alkm slm w rhmtul Laah._
Kalmar Mazhaba tana da ma’anoni guda biyu a wurin malamai. Sukan yi amfani da ita da ma’anar aqida, kamar inda suke cewa: ‘Mazhabar Ashaa’irah shi ne: Imani da Siffofin Allaah guda bakwai kaɗai’, ko kuma cewa: ‘Fifita Aliyyu a kan sauran _Khulafaa’ur Raashiduun_ ita ce: Mazhabar Shi’a.’
Wani lokaci kuma malamai sukan yi amfani da kalmar mazhaba suna nufin: Fahimtar da wani malami daga cikin malaman Fiqhu na Ahlus-Sunnah ya ɗauka a kan wata mas’ala da ijtihaadinsa (ƙoƙarinsa). Kamar yadda suke cewa: ‘Mazhabar Abu-Hannefah ko Maalik ko As-Shaafi’iy ko Ahmad ko Daawud a kan mas’ala kaza ita ce kaza da kaza.’ Suna nufin abin da ya zaɓa kuma yake gudana a kansa a fahimatarsa ga nassoshi ko ƙa’idojin shari’a.
Yawancin mabiya Shi’a sun san cewa gama-garin Ahlus-Sunnah ba su san wannan bambancin ba, don haka sai su riƙa amfani da kamar a dunƙule da manufar ɓad-da-bami. Ta yadda mai sauraronsu zai ɗauka ma’anar mazhaba ta biyu suke nufi, alhali kuwa su ma’anar ta farko ce suke nufi a lokacin da suka ce: Shi’a mazhaba ce.
Abu ne sananne a wurin ɗaliban ilimi cewa: Bambancin mazhaba a tsakanin malaman Fiqhu na Ahlus-Sunnah ba ya halatta ya janyo matsala ko rikici. Domin alal misali, wane bahambale ko bazaahire ne a yau zai ƙyamaci yin sallah a bayan Al-Imaam As-Shaafi’iy ko Al-Imaam Maalik _(Rahimahumal Laah)_ don ya ga ya ci naman raƙumi, kuma bai sake alwala ba?!
Amma babu ko tantama duk wani musulmi mai imani da taqawa yana jin nauyi - in ba zafi ba ma - a cikin zuciyar idan ya ji fatawar da take halatta yin sallah a bayan duk wanda aka san yana da aqidar zagin _Khalifatur Rasuuli:_ Abubakar ko _Amirul-Mu’mineen_ Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa),_ balle duk wanda yake da aqidar zargin _Ummul-Mu’mineen_ A’ishah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ a kan abin da Alqur’ani Mai Girma ya riga ya wanke ta!
Wannan ya sa wajibi ne ’yan uwa Ahlus-Sunnah su ƙara mayar da hankali da zurfafa bincike da fahimtar *Fiqhul-Akbar* da ya shafi aqida da Tauhidi fiye da *Fiqhul-Asgar* da ya shafi mas’alolin *Furu’a* na ibada da Mu’amala.
Daga cikin bambancin da malamai suka fayyace a tsakanin Ahlus Sunnah da mazhaba (aqidar) mabiya addinin shi’a *(Ar-Raafidah)* akwai waɗannan:
(i) *Alqur’ani:*
Ahlus-Sunnah sun yarda cewa Alqur’ani saukakken Littafi ne tsararre, wanda babu wani sauyi ko ƙari ko ragi da zai iya shiga cikinsa tun daga saukarsa har zuwa yau, kuma har zuwa Tashin Ƙiyama.
A wurin ’yan shi’a kuwa suna ganin akwai sauye-sauye na ragi ko ƙari da wai aka shigar a cikinsa daga bayan rasuwar wanda aka saukar masa da shi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)!_
(ii) *Hadeeth:*
A wurin Ahlus-Sunnah, Hadisi ko Sunnah shi ne mattarar fassara ko ƙarin bayanin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi ga Alqur’ani. Ya ɗauki tsawon shekaru ashirin da uku da ƙarshen rayuwarsa yana yin wannan bayanin. Babu wani hadisin da ake yarda a yi aiki da shi sai ya cika sharuɗɗan inganci da malaman hadisi suka sanya tun farko, kamar hadisan da su ke cikin Sahih Al-Bukhaariy da Sahih Muslim da makamantansu.
A wurin mabiya shia’a kuwa ba su amincewa da hadisi sai in ya dace da ra’ayoyin malaman mazhabar su (aqidarsu), ko kuma sai in daga hanyar limaman mazhabarsu (aqidarsu) aka riwaito shi. Ba su yarda da Sahih Al-Bukhaariy ko Sahih Muslim ba, balle sauran littaffan da suke ƙasa da su a wuri inganci.
(iii) *Sahabbai:*
Ahlus-Sunnah suna darajawa da mutunta Sahabban Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ suna fifita fahimtarsu da ra’ayinsu a kan ra’ayi ko fahimtar wanda ba su ba. Domin su ne suka halarci yanayi da lokutan da aka saukar da dokokin shari’a. Suna fifita *Al-Khulafaa’ur-Raashiduun* a kan sauran sahabbai. Saɓanin da ya shiga tsakaninsu ba ya janyo zargi ko suka ga wani ɗaya daga cikinsu. Su masu ijtihadi ne, waɗanda suke a tsakanin lada guda ɗaya da lada biyu. Allaah ya ƙara musu yarda gaba-ɗayansu.
A wurin mabiya shi’a kuwa suna gani dukkan sahabbai, in ban da ’yan kaɗan kamar biyar ko shida, duk sun yi ridda a bayan rasuwar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)!_ Kuma ba su ganin wani da girma fiye da Aliyu Bn Abi-Taalib _(Radiyal Laahu Anhu)._ Duk wanda ya hau karaga halifanci kafin Aliyu suna ɗaukarsa ko dai azzalumi ne ko kuma ma kafiri! Haka sauran limamai daga cikin zuriyarsa.
(iv) *Tawheed:*
Ahlus-Sunnah suna tsarkake Allaah Ta’aala, suna kaɗaita shi da nau’ukan bauta, ba su haɗa shi da komai a cikin ibadarsa. Shi kaɗai suke roƙo a cikin sauƙi da tsanani domin neman ya bayar da alkhairi kuma ya kawar da damuwa da baƙin ciki. Domin shi kaɗai ne maƙagin halittu kuma mai iko a kan dukkan komai.
‘Yan shi’a kuwa, kodayake sun yarda Allaah Makaɗaici ne, amma kuma suna haɗa waɗansu limamansu da shi a wurin addu’a, inda suke cewa: Ya Aliyyu! Ya Hussaini! Suna yin alwashi da yanka da ɗaura sirdi don ziyarar ƙabrukan limaman, da sauran ayyukan shirka!
(v) *Ahlul-Baiti:*
A wurin Ahlus-Sunnah dukkan musulmi na kirki mai taqawa da tsoron Allaah yana daga cikin Ahlur-Rasuul. Amma keɓantattun Ahlul-Baiti sun haɗa dukkan muminai daga cikin danginsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ kamar na cikin Banu-Haashim da Banu-Abdilmuttalib.
A wurin ’yan shi’a kuwa Ahlul Baiti su ne: Aliyu da Faatimah da Al-Hassan da Al-Hussaini da jikokin Al-hussaini kaɗai!
(vi) *Shari’a da Hakikah:*
Ahlus-Sunnah suna ganin Shari’a ita ce dai haƙiƙah, domin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ bai bambanta ba a tsakaninsu, kuma bai ɓoye wani abu domin waɗansu keɓantattu daga cikin al’ummarsa ba. A kan haka ya dawwama har zuwa lokacin da Ubangiji Ta’aala ya kammala masa addininsa kuma ya cika masa ni’imarsa. Bai halatta a saɓa wa dokokin shari’a na zahiri da da’awar bin haƙiƙa ta baɗini ba.
Su kuwa mabiya shi’a suna ganin akwai bambanci a tsakanin shari’a, watau dokokin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya zo da su domin gama-garin musulmi, da kuma haƙiƙa watau wani keɓantaccen ilimi da fahimta da ya keɓance keɓantattun Limamai da su. Kuma suna iya saɓa wa dokokin shari’a na zahiri da hakan!
(vii) *Fiqhu:*
Ahlus-Sunnah suna gina ayyukan ibada da mu’amalarsu daga irin abin da nassoshin Alqur’ani da Sunnah Sahihiya suka kawo ne, a bisa dacewa da fahimtan malaman farko daga cikin Sahabbai da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa. Zuwa ga maganganunsu da ƙa’idojin da suka shimfiɗa ne ake komawa don warware sababbin matsalolin da suka ɓullo wa al’umma.
Su kuwa mabiya shi’a ga Limamansu magada ilimin haƙiƙa suke komawa don warware sababbin mas’aloli. Kuma suna da ƙa’idar saɓa wa fatawoyi da ayyukan Ahlus-Sunnah a duk lokacin da suka samu sararin yin haka, kamar idan suka rasa fatawa daga wani limaminsu a kan kowace mas’ala. _(Khutuutul Areedah na Muhibbud-Deen Al-Khateeb (Rahimahul Laah, shafi: 212-217))_
A taƙaice dai akwai manyan bambance-bambance da mabiya shi’a suka ƙirƙiro kuma suka saɓa wa Sahabbai da Tabi’ai da su, waɗanda wasunsu suke kore imanin mai amincewa ko yarda da su. Kamar maganar da wani daga cikin manyan malamansu: As-Sayyid Ni’imatul-Laahi Al-Jazaa’iriy inda yake magana a kan haƙiƙanin addinin ’yan Shi’a Imaamiyyah da kuma dalilan da suke wajabta a kama bin saɓanin abin da Ahlus-Sunnah suke a kansa, inda yake cewa:
إِنَّا لَا نَجْمَعُ مَعَهُمْ - اَيْ مَعَ السُّنَّةِ - عَلَى إِلَهٍ ، وَلَا عَلَى نَبِيٍّ ، وَلَا عَلَى إِمَامٍ ، وَذَلِكَ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ : إِنَّ رَبَّهُمْ هُوَ الَّذِي كَانَ مُحَمَّدٌ نَبِيَّهُ وَخَلِيفَتُهُ مِنْ بَعْدِهِ أَبُوبَكْرٍ . وَنَحْنُ لَا نَقُولُ بِهَذَا الرَّبِّ وَلَا بِذَلِكَ النَّبِيِّ ، بَلْ نَقُولُ : إِنَّ الرَّبَّ الَّذِي خَلِيفَةُ نَبِيِّهِ أَبُوبَكْرٍ لَيْسَ رَبَّنَا ، وَلَا ذَلِكَ النَّبِيُّ نَبِيِّنَا
Haƙiƙa! Mu ba mu haɗu da su (Ahlus-Sunnah) a kan wani abin bauta, ko a kan wani annabi, ko a kan wani limami ba. Domin kuwa su cewa suke yi: Ubangijinsu shi ne wanda Muhammadu ne Annabinsa, kuma halifansa a bayansa shi ne Abubakar. Mu kuwa ba mu yarda da wannan Ubangijin, ko wannan Annabin ba. Abin da muke cewa (muke yarda da shi) dai kawai shi ne: Haƙiƙa! Wannan Ubangijin da Halifan Annabinsa shi ne Abubakar ba Ubangijinmu ba ne, kuma wannan Annabin ba annabinmu ba ne! _(Al-Anwaarul Jazaa’iriyyah: 2/278)_
Tun da dai abu ne tabbataccen a tarihi a wurin kowa cewa: Abubakar As-Siddiq _(Radiyal Laahu Anhu)_ shi ne khalifan Manzon Allaah a bayan rasuwarsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ kenan wannan maganar ta tabbatar da cewa: A wurin Al-Jazaa’iriy: Mabiya shi’a ba su amince da Allaah Ubangijin Halittu ba, kuma ba su yarda da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ kenan! _(Dubi maganar As-Sayyid Husain Al-Muusawiy a cikin Lil Laahi Thumma Lit-Taareekh, shafi: 85)._
Don Allaah! Dubi yadda baƙar ƙiyayyar da suke yi wa Abubakar As-Siddiq _(Radiyal Laahu Anhu)_ ta kai su ga furta abin da yake kai su ga mummunar taɓewa!
Allaah ya kiyashe mu.
_Wal Laahu A’lam._
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*