ZAN IYA YIN SALLAH SHAFA'I DA WITRI A ZAUNE?
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT
*TAMBAYA* ❓
Assalamu alaikum
Malam barka da rana Allah kuma Yaqarama lfy
Tambayata malam nakasance ina aikin gida sosai da xaran dare yayi xanji ba abunda nake da buqata sai bacci hatta gabbaina duk agajiye suke Wanda ko sallah xanyi dakyar nakeyi wato sallar ishsha amma dai ina kokari inayi atsaye toh amma fa shafa"I da wutiri bana iyayi atsaye malam sai a zaune shin Allah xai qarba kuwa
*AMSA* 👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
SALLAH a zaune tana inganta a nafila, kuma yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye, saboda fadin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan ya yi sallah a tsaye wannan shi ya fi. Wanda kuwa ya yi sallah a zaune to yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye, wanda kuwa ya yi sallah a kwance to yana da rabin ladan wanda ya yi a zaune” [Bukhari ne ya rawaito shi].
Idan kuwa ya yi sallah a zaune saboda uzuri to yana da lada cikakke, saboda faÉ—in Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan bawa ya yi rashin lafiya ko ya yi tafiya, za a rubuta masa (ladan) abin da yake aikata wa idan yana nan (bai yi tafiya ba) ko kuma idan yana da lafiya” [Bukhari ne ya rawaito shi].
Sallah a zaune bata inganta a farillah in dai zai iya tsayuwa.
SALLAR FARILLAH wajibi ne a yi ta a tsaye, saboda yin sallah a tsaye rukuni ne daga cikin rukunnan sallah, ba makawa sai mutum ya yi ta, amma yin sallah a zaune ga wanda ba shi da lafiya, ko ba shi da ikon yin tsayuwar, wannan babu laifi idan ya yi sallah a zaune, saboda ya tabbata daga sahabin Annabi ï·º
Imrana É—an Husaini Allah ya qara masa yarda ya ce:
Na kasance ina fama da basir, sai na tambayi Annabi ï·º game da yadda zan yi sallah, sai ya ce mani: "Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba ka yi a zaune, idan ma ba za ka iya ba ka yi a kan É“arin jikinka (wato a kwance)". Bukhariy 1117.
Wannan dalili ne a kan yin sallah a zaune ga mare lafiyan da ba zai iya yin ta a tsaye ba, ko kuma ga wanda tsayuwar take masa tsananin wahala kamar wanda ya tsufa tukuf da makamantan haka. Amma lafiyayyen mutum, wanda yake da ikon yin sallah a tsaye, idan ya yi ta a zaune sallarsa ba ta inganta ba.
Allah ne mafi sani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕