*MAKARANTAR AZUMI 005//*
📌 _LOKUTAN AZUMI_
Lokacin Kame-baki da bullowar Alfijir;
Abu na farko dai abunda a Yau aka sani da lokacin kame-baki, shine a tsaya daga cin sahur da wasu Æ´an lokuta, yin haka Bidi’a ne, saboda bashida dalili a Littafin Allah ballantana Sunnar Annabi SAW, hakan ya haifar da mummunar bidi’ar nan ta hana ma mutane cin abinci tun daga lokacin har zuwa É“ullowar alfijir, wanda kuwa shari’a ma tazo ne da halatta sabanin haka na jinkirta yin Sahur.
Hadisi ya inganta Imamul Hakim ya fitar a cikin Littafin shi, Manzon Allah SAW Ya ce: “idan É—ayanku yana tsaka da cin abinci, sai aka kira Sallah, to ya cigaba da cin abincin sa kada ya ajiye har sai ya gama biyan buÆ™atar sa”.
_Lokacin BuÉ—a-baki_
Abunda ake so ga mai azumi shine ya gaggauta BuÉ—a-baki, don ya zama yayi cikakken koyi da shiriyar Annabi SAW, domin babu shiriyar da ta kai ta Annabi SAW.
Gameda lokacin BuÉ—a-baki kuwa; babu wata alama da za’a ce an sanyata wacce da itane ake gane lokacin shan-ruwa yayi sai alama wacce take Allah Ya sanyata, itace; faÉ—uwar rana, da faÉ—uwar wainar ta a Yamma, da bayyanar duhu-duhun dare daga gabas, da juyawar yini ta É“angaren Yamma; koda akwai sauran hasken yini.
SaÉ“anin wannan Bidi’a ce da wasu suka Æ™irÆ™iro, saboda barin su ga shiriyar Annabi, basa shan ruwa sai dare ya gama yi taurari sun fito, ga wahalar yunwa da suka É—aukar ma kansu, don Annabi SAW cewa yayi da zaran rana ta faÉ—i to lokacin shan ruwa yayi, hadisi ne ingantacce da Bukhaariy da Muslim suka riwaito shi.
Sannan ƙara wasu ƴan lokuta na yin farilla aqi yin Buɗa-baki, duk wannan ɗaukar ma kai ne da zaqewa cikin Addini.
*Mas’ala* : da ace mai Azumi zai yi buÉ—a-baki, tsammanin shi rana ta faÉ—i, daga baya ta bayyana gareshi ashe bata faÉ—i ba, abunda yafi rinjayen dalili shine zai cigaba da azumin shi, kuma bazai yi wata ramuwa ba, saboda makamanaciyar irin wannan ta taÉ“a faruwa a zamanin Annabi SAW, kuma bai musu umarni da ramuwa ba.
✍ *ANNASIHA TV*