AL’AMURAN DA BASU DA TASIRI WAJEN INGANCIN AZUMI

*MAKARANTAR AZUMI 010* //



 *AL’AMURAN DA BASU DA TASIRI WAJEN INGANCIN AZUMI* 

Anan wasu al’amura ne waɗanda suka halasta ga mai Azumi yayi su batare da sun bama Azumin shi wata matsala ba, wasu al’amuran kuma basa halasta yayi su, sai dai da ace zai yisu to Azumin shi baya baci saboda hakan, wasu al’amuran kuma da wasu Mutane suke bayar da Fatawa akan su cewa wai suna bata Azumi, to a gaskiya ba haka al’amarin yake ba; saboda ba a samu wani dalili akan haka ba wanda zasu iya dogaro akanshi ba; na daga ciki;

1-   Yin Asuwaki a kowani lokaci koda da rana tsaka ne ana Ramadana, misali yin Brush da Makilin duka waɗannan basa bata Azumi.

2-   Kur-kurar baki da kuma shaƙar Ruwa amma batare da kaiwa matuka ba wajen yi, shima baya ɓata Azumi; saboda abunda Annabi yace ma wani Sahabi: “ka kai matuka wajen kur-kurar baki, sai dai idan ya kasance kana Azumi ne to ba zaka kai matuƙa ɗin ba”

3-   Sanya Tozali ko kuma Maganin ciwon Ido ko Kunne, koda kuwa ana iya jin ɗanɗanon su a cikin Maƙoshi suma dukansu basa ɓata Azumi.

4-   Ɗanɗana abinci; amma da sharaɗin kada a barshi ya kai zuwa ga ciki, kenan da zaran ya dandana sai ya tofar, saboda fatawar Abdullahi dan Abbas da tazo akan halascin haka.

5-   Sumbanta da runguma: anan da Tsoho da Matashi duk hukuncin su daya, amma idan har hakan bazai kai su ga abunda aka Haramta ba; shine Jima’I wanda kai tsaye yake bata Azumi, kuma yana wajabta ramuwa ne tare da Kaffara. Dalilin akan haka shine abunda Nana A'isha (Allah ya kara mata yarda) take cewa: "Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sumbanta yana runguma alhali yana mai Azumi, sai dai shi Manzo Allah ﷺ yana mallakar kansa" 
[Bukhaariy ne ya ruwaito shi]

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)