AN FARA CIRE SLIP NA JARABAWAR MOCK


•√An fara Cire Slip din Jarrabawar Mock

•Har yazuwa yanzu ba'a rufe Sayar da lambobin yin rijistar Jarrabawar Jamb na e-PIN ba, duk da wa'adin yau da hukumar ta bayar a matsayin ranar da za'a rufe

•√Adadin Daliban da sukayi rijistar Jamb UTME sun kai kimanin Dubu Dari Takwas da Arba'in da Biyar, a yayin da wadanda sukayi rijistar Jamb Direct Entry kuwa suka kai Dubu 35, zuwa Yammacin jiya Lahadi



   ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••



•√ A cikin Jadawalin Jamb bulletin da hukumar Jamb ta fitar a yau Litinin, hukumar ta bukaci dukkannin Daliban da sukayi rijistar jarrabawar Mock, dasu Ziyarci shafin hukumar dan su cire Slip din jarrabawar su, domin sanin Cibiyoyin da zasu rubuta jarrabawar dakuma lokacin da ake bukatar su Ziyarci Cibiyoyin rubuta Jarrabawar, wacce ake Shirye-Shiryen Gudanarwa a ranar 20 ga wannan Watan na Mayu da muke ciki, domin kuwa tuni Anfara cire Slip din jarrabawar daga shafin hukumar Jamb tun a jiya Lahadi 9 ga wannan Watan da muke ciki kamar yadda hukumar ta bayyana.


•√ Hakika Dalibai da dama sun shiga rudani tareda dumbin Alhini tun bayan da hukumar Jamb ta bayyana Yau Litinin 10 ga Watan da muke ciki a matsayin ranar da zata rufe sayar da lambobin rijistar Jarrabawar da Akafi sani da e-PIN, Saboda matsalar da suke fama da ita ta rashin turo musu lambobin Profile Code daga hukumar ta Jamb wanda dasune akanyi amfani wajen sayen lambobin e-PIN, Saidai kuma a wani Mataki na tausayawa Daliban, hukumar ta Jamb har yazuwa yanzu bata rufe sayar da lambobin na e-PIN ba kamar yadda ta bayyana cewar zata rufe a yau, Saidai kuma har yazuwa yanzu hukumar bata bayyana cewar ko ta kara wa'adin zuwa wani lokaci na daban ba, duk da kasancewar dai bata rufeba, Saidai ana Saran sanin Matakin da hukumar ta dauka na tsawaita wa'adin ko akasin haka da zarar hukumar ta kammala zaman da ta shirya gudanarwa a Yau Litinin 10 ga Watan Mayu, tareda manyan-manyan Shuwagabannin hukumar dakuma Daraktocin ta.


•√Haka zalika a cikin Jadawalin na Jamb bulletin, hukumar Jamb ta bayyana cewar har zuwa Yammacin Jiya Lahadi kimanin Dalibai 845,517 ne sukayi rijistar jarrabawar Jamb UTME, a yayinda Dalibai 38,886 kuwa sukayi rijistar jarrabawar a tsarin Direct Entry (D.E).


    ASOF tana shawartar ku daku kwantar da hankulanku, Insha'Allahu kyakyakyawan labari yana tafe.



Daga : Miftahu Ahmad Panda (PRO ASOF JAMB ONLINE ORIENTATION COMMITTEE).

      08039411956


@ASOF 2021
Post a Comment (0)