*MAKARANTAR AZUMI 019* //
📌 _RAMUWAR AZUMI_
*Na farko* : an so ga wanda ramuwar wasu kwanaki na Watan Ramadana suke akan shi, da yayi gaggawa zuwa ga ramuwar a yayin da ya samu ikon yin haka, domin haka shine ya dace da nassoshi gamammu da suke nuni akan haka, kamar fadar Allah: ((kuyi gaggawa zuwa ga samun Gafara daga wurin Ubangijin ku)) [Suratu Ali-Imrana: 133), sai dai kuma koda ya jinkirta ramuwar har zuwa wani Ramadan din mai zuwa, kai koma zuwa shekaru biyu ne babu komai akan shi sai ramuwa kadai; tunda har Allah bai kayyade iya lokacin da za’ace idan bai rama ba yayi laifi, kadai dai Allah ya wajabta mishi ramuwa ne, a inda Allah yace: ((sai ku rama a wasu kwanakin)) kuma bai zo a cikin Sunnar Annabi (SAW) abunda zai iyakance ramuwar da wani lokaci sananne ba, duk kuwa wanda ya iyakance shi da wani lokaci, ko kuma yace za’ayi ramuwar ne tare da ciyarwa (saboda jinkirta wa da akayi) to sai yazo da dalili.
*Na biyu* : dai-dai ne yayi ramuwar a jere ko kuma a rarrabe, saboda Allah ya wajabta ramuwa ne kai tsaye: ( *(sai ku rama a wasu kwanakin* )) kuma bai inganta daga Annabi (SAW) gameda haka ba har abada.
*Na uku:* duk wanda ya mutu kuma akwai Azumin Ramadana akanshi to ‘yan uwan shi baza su biya masa wannan Azumin ba, sai dai kuma duk wanda yace akwai halascin rama masa wannan Azumin, yana mai kafa Hujja da maganar Annabi (SAW): “ *Duk wanda ya mutu akwai bashin Azumi akanshi, Waliyyin shi yayi masa wanann Azumin* ” to ba abun a sallama mishi bane akan haka, saboda Hadisin ya zo ne game da Azumin Alwashi kamar yadda Malamai sukayi bayani, sai dai kuma wasu daga cikin ma’abota Ilimi sun tafi akan abunda yake kawai akan shi, shine ayi masa ciyarwa ta isa, a kowace Rana Miskini daya, wannan itace fatawar manya daga cikin Sahabbi kamar Uwar Muminai Nana Aisha da Babban Malamin Tafseerin nan Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara musu yarda, Amin.
✍ *ANNASIHA TV*