AZUMIN KWANAKI SHIDA A WATAN SHAWWAL


*AZUMIN SITTU SHAWWAL* 
 
📌 ```AZUMIN KWANAKI SHIDA A WATAN SHAWWAL:``` 
 
Allah Ya shar'anta Azumtar kwanaki Shida a cikin Watan Shawwal. Wata ne mai girman Daraja, ana ma Æ™irga shi a Wata na farko cikin Watannin Aikin Hajji, kuma an shar'anta Ibadoji a cikin shi ta É“angaren Azumtar kwanaki Shida a cikin shi, Imamu Muslim ya fitar da Hadisi a cikin ingantaccen littafin shi daga Sahabi Abu Ayyubal Ansariy - Allah ya kara masa yarda -, Manzon Allah (S.A.W)- yace: " *Duk wanda ya azumci Watan Ramadana ya biyo bayan shi da azumin kwanaki Shida a cikin Watan Shawwal, ya kasance kamar ya Azumci Shekara ne".*  
 
 *HUKUNCIN AZUMTAR KWANAKI SHIDA A WATAN SHAWWAL:* 
 
An shar'anta wannan Ibada ne bayan Azumin Watan Ramadana, aka shar'anta Azumin kwanaki Shida a cikin wannan Wata, Malamai sun tattauna gameda hukuncin wannan Azumi, sai suka tafi zuwa ga maganganu guda biyu, ga bayanan su: 
 
 *_Magana ta farko_* : wasu suka tafi akan; Azumin Sittu Shawwal Mustahabbi ne, suna masu kafa hujja da Hadisin Abu Ayyubal Ansariy da muka ambata a sama, suka kuma Æ™ara da Hadisin da aka ruwaito daga Sahabi Thauban, daga Manzon Allah (S.A.W) Ya ce: " *_Azumin Watan_ _Ramadana yana daidai_ _da Azumtar Watanni_ _Goma_* *_ne, shi kuma_ _Azumin kwanaki Shida a_ _bayan shi daidai yake_ _da Azumtar_ _Watanni Biyu, wannan_ _shine yake daidai da_ _Azumtar Shekara_* 

Kuma na daga cikin abunda yake kara Æ™arfafa falalar Azumin kwanaki Shidan a cikin Watan Shawwal, suna masu kafa hujja da faÉ—in Allah:- (Duk wanda yazo da aiki kyakkyawa to yana da Lada kwatankwacin sa linki Goma. *Duk kuwa wanda yazo da mummunan aiki to za'a sakankan masa ne kaÉ—ai da irin abunda ya aikata na Zunubi, ba tare da an zalunci kowanne daga cikin su ba).* 
 
Wannan Aya tana game bayani ne akan duk wani kyakkyawa da Mutum ya aikata ana masa sakamako ne da linki Goma na Lada kwatankwacin sa, sai dai Azumi za'ayi togaciwar sa da faɗin Annabi (S.A.W) daga Allah (S.W.T):- " *_Dukkan aikin ɗan Adam_ _nashi ne, sai dai_ _Azumi kaɗai, shi kam_ _nawa ne, Ni ne zanyi_ _masa sakamako, na_ _rantse da Wanda ran_ _Annabi (S.A.W) yake a_ _hannun Sa, warin bakin_ _mai Azumi yafi Almiski_* *_ƙamshi a wajen Allah_ _ranar Al-Qiyamah_*

 *_Magana ta biyu_ :* wasu kuma sun tafi akan Karhancin yin wannan Azumi, wato abun Æ™yama ne yin sa, saboda abunda ya zo daga riwayar Yahaya É—an Yahaya ta littafin Muwatta; rashin samuwar wani nassi da yazo daga wajen Malamai ma'abota Ilimi da Fiqihu da kuma magabata da yake nuni akan sun Azumci waÉ—annan kwanaki Shida a cikin Watan Shawwal bayan Watan Ramadana; saboda tsoran kada ya zama Bidi'a ne wato Æ™irÆ™irar shi akayi, kuma Jahilai na iya É—aukan wajabcin Azumin. 
 
Sai dai, Malami sun bayar da amsa kan wadannan maganganu, a taÆ™aice: 
 
 *Amsa ta farko* : Tunda Hadisin ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) to babu batun wani Malami bai yi aiki dashi ba, kamar yadda Imamun Nawawiy yake faÉ—a, indai Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah to babu batun Malam wane baiyi aiki dashi ba tunda har ya tabbata. 
 
 *Amsa ta biyu* : Malamai sukace ai tunda har akwai bikin Sallar Idi da akeyi to babu ta yadda za'ayi Mutum ya É—auki Azumin Sittu Shawwal yana haÉ—e ne da Watan Ramadana. 
 
 *TANBIHI* : Ba'a azumtar Ranar Asabar a cikin kwanaki da Mutum ya zaÉ“a zai yi wannan Azumi, koda ya azumci Ranar Juma'ah, saboda Annabi SAW Ya hana azumtar Ranar Asabar koda kuwa yana da wani sababi, kamar wannan da za'ayi, don haka babu Æ™irgen Ranar Asabar a wannan Azumi. 
 
Kenan, anan babu ta yadda za'ayi a É—auki Fatawar su Imamu Malik, tunda tayi karo da Hadisi da ya tabbata daga Manzon Allah, muna roÆ™on Allah Ya gafarta ma Imamu Malik, Amin." 
 
 *✍ ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)