AZUMIN 'SITTU SHAWWAL'
Al-Imamu Ahmad da Muslim da Abu Dawud da Timiziy da Nasà'iy da Ibn Majah da Baihaƙiy da wasunsu sun ruwaito hadisi daga Abu-Ayyub Al-Ansariy (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: duk wanda ya azumci watan Ramadan sannan ya biyo baya da azumi guda shida a watan Shawwal to za a ba shi ladan azumin shekara ɗaya".
Baya ga wannan riwaya ta Abu-Ayyub Al-Ansariy, Al-Imamut Timiziy ya yi ishara zuwa ga riwayar Jabir (Ɗabarani a Al-Mu'ujamul Ausaɗ) da Ibn Umar (Ɗabarani a Al-Mu'ujamul Kabeer da Ausaɗ da isnadi mai rauni ƙwarai) da Thauban (Ibn Majah) da Abu -Huraira (An-Nàsik wal Mansook na Al-Athram).
A ƙarƙashin wannan hadisi da ma wasu Hadisan da ke da alaƙa da wannan mas'ala, malamai suka ce:
1. Mustahabbi ne yin azumin kwanaki shida a watan Shawwal.
2. Ramuwar azumin Ramadan ga waanda ake bin shi wani sashe na azumin Ramadan ɗin shine abin da ya kamata a fara yi.
3. Ana iya fara yin azumin Sittu Shawwal tun daga 2 ga watan Shawwal.
4. Ana iya yin su a jere, ko a rarrabe, gwargwadon hali.
5. Za a iya yin azumin a ranakun da aka hana ware su da azumi, kamar juma'a, amma in an haɗa ta da Alhamis ko Asabar.
6. Bai halasta ba ga matar aure ta yi azumin nafila matuƙar mijinta na gari sai da izinin sa.
7. Ga wanda ya shagaltu da ramuwar azumin Ramadan har Shawwal ya ƙare zai iya yin Sittu Shawwal a Dhul-Ƙa'adah.
Allah Ubangiji shine mafi sani.