ANA BUGUN JAKI ANA BUGUN TAIKI👉 BA SOKE KAYAN LEFEN BA WANE HUKUNCI AKAI GA MASU SAKIN AURE BA DALILI.
DAGA
MUHAMMAD SALISU MUHAMMAD SEEKER DUTSE.( National Director Innovation and Strategic Arewa Media Writers).
Aure bautar Ubangiji, haka ma sakin auren shi ya halatta yin sa amma ta hanya mai kyau. Ina fadar haka ne sakamakom matakan da naga hukumomi suna dauka na soke kayan lefe da wasu wahalhalu da suke sanya auren yake tsada.
Sai dai bincke ya nuna Qabila guda ce a duniya tafi Bahaushe sake-saken aure wato wata Qabila da take Qasar Indiya, Wanda anawa ganin ba soke lefen ne kadai yake buqatar doka ba, shi kansa sakin auren yaci ai masa doka da Kuma amfani da takardar shaida rabuwa kamar yadda ake gabatar da ta gwajin lafiya. Wato Hukuma ta miqa sashe na musamman da zai saurari sakin aure ta hanyar wannan takardar shaidar rabuwa kafin a rabu ,duk wanda bai zo ba wajen bayyan a hukumance yanda aka bashi aure zai saki to a hukunta shi ba bata lokaci.
Muna fakewa da musulunci muna abinda muka ga dama , addinin musulunci addini ne mai tsari da komai ya fadi yadda yadda za ai. Amma daga anyi magana kace Yahudanci ne in za a bi (Official Declaration ) ai ba na musulmi bane, injiwa kaje kayi bincike akan (Islamic Civilisation) kaji yadda musulunci yake da tsari da tafiya da zamani.
A baya tsohon Sarkin Kano ,Kuma tsohon Shugaban Babban Bankin Qasar nan Malam Sunusi Lamido Sunusi II ya kawo wannan ra'ayi akai ta sukarsa kuma gaskiya ne wallahi .
Tunda yanzu anyarda hukuma ta shiga lamuran wahalar aure to wajibinta ne ta Kuma samar da tsari wajen ya kuma sakin auren zai kasance kar Kuma garin gyaran gira a bata idanu.
Wato kowanne bangare a bashi takardar raba aure wato (Divorce certificate ) Kuma ta kasance tana da tsari da doka wajen karbar auren, ta hanyar sa hannun mai yin auren , Limamin da ya daura auren da Kuma mai unguwar da yake wakiltar wannan yanki da aka daura auren.
Hakan shi zai bawa hukuma damar duk wanda sauqin auren yasa ya saki wata to akwai doka bazai sakin ba sai ya zo gaban hukuma da wannan takardar shaidar saki ya fadi dalilan sakin , in yana da hujjoji sai a saka a bashi dama yai saki , in kuwa aka samu sauqin auren yasa shi iya shege , sai a dakatar dashi in yaqi sai a barshi yai sakin sai doka tai aiki akansa cewa duk 'yar da yaje ya qara aurowa hukuma tana sane dashi ga hukuncinsa tunda saki yake ba dalili. Ina ganin ba soke lefen ba wane mataki aka dauka ga Wanda suke wasa da aure kamar cire riga haka suka maida korar mace da qara auran wata sabida yana gadara da kudi bare yanzu ance ga sauqi ya samu.
Wannan dalilin yasa muke Kira ga duk wata hukuma da ba ga lefen ba har sakin auren hankalinsu ya kamata yakai wato (Ana bugun Jaki ana bugun taiki). Allah sa mahukunta su duba wannan matsalar da ake fama da ita ba iya waccan ba.@ SEEKER DUTSE ( NATIONAL DIRECTOR INNOVATION AND STRATEGIC AREWA MEDIA WRITERS).