FALALAR SURATUL KAHFI ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻜﻬﻒ )
*TAMBAYA*❓
Salm INA kwana ya gida
Dan Allah inason sanin Falalan suratul Khaf
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Hakika dukkan surorin alqurani suna da falala wajan karantawa da aiki da su,amma Allah da Manzonsa s.a.w sun bayyana mana wasu surorin sunfi wasu surorin falala,kamar yadda wata ayar tafi wata ayar falala,Manzon Allah s.a.w ya bayyana mana Suratul Fatiha itace mafi girma sura acikin Alqurani mai girma,haka kuma Ayatul Kursiyu itace aya mafi girma acikin ayoyin alqurani mai girma baki daya.
Suratul Kahf tana da falala mai girma wajan karantata da aiki da abinda yake cikinta,kamar yadda hakan ya tabbata daga Manzon Alllah s.a.w da kuma abinda aka ruwaito daga Sahabbansa suna fada game da wannan sura mai girma.
1-Wanda ya hardace ayoyi goma na farkon suratul Kahf, zai sami kariya daga fitinar Dujal.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Dukkan wanda ya hardece ayoyi goma na farkon suratul Kahfi,anyi masa kariya daga Dujal).
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ( 809 )
A wani Hadisin Annabi ﷺ yana cewa:
(Dukkan wanda ya kiyaye ayoyi guda goma na farkon Suratul Kahfi an kareshi daga fitinar Dujal).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ - ﺭﻗﻢ : ( 4323 )
2-Wanda yake karanta suratul Kahfi Allah yana bashi wani haske har zuwa ranar alqiyama.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Wanda ya karanta suratul Kahfi,yana da wani haske har ya zuwa ranar alqiyama,haske daga inda yake zuwa makka,wanda ya karanta ayoyi goma na karshen surar,sannan Dujal ya bayyana,bazai cutar da shi ba......).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ( 225 )
3-Karanta suratul Kahfi a Daren juma'a Allah zai bashi wani haske.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Wanda ya karanta Suratul Kahfi a daren Juma'a,Allah zai bashi wani haske a tsakaninsa da Baitil Ateeq).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ( 736 )
4-Wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar juma'a,Allah zai bashi wani haske daga wannan juma'ar zuwa wata juma'ar.
Manzon Allah ﷺ yace:
(Wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar Juma'a,Allah zai bashi wani haske daga wannan juma'ar zuwa wata juma'ar).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ( 736 )
Allah ne mafi sani
Allah kasanya mu cikin masu samun wadan nan falaloli.