GWARGWADON ABUNDA AKE FITARWAR A ZAKKAR KONO (FIDDA-KAI)



*MAKARANTAR AZUMI 027* //
 
📌 ```GWARGWADON ABUNDA AKE FITARWAR A ZAKKAR KONO (FIDDA-KAI)``` 

Musulmi zai fitar da Sa’i ɗaya na Abinci daga cikin na’u’o’in da bayanan su ya gabata. 

Sa’i abun lura anan shine Sa'in Mutanen Madina, saboda Hadisin Abdullahi ɗan Umar wanda a ciki yake ambata irin Sa'in (Albaniy ya inganta shi a Silsilatul Ahadeethus Saheehah). 

 *SUWA AKE FITARWA?* 

Musulmi zai fitar da ita wa kansa da kuma duk wanda yake ɗaukan ɗawainiyar sa, Ƙarami da Babba, Namiji da Mace, Ɗa da kuma Bawa, saboda Hadisin Abdullahi ɗan Umar wanda Albaniy ya inganta shi a littafin Irwa'ul Ghalil; Lambar Hadisi na 830. 

 *WAƊANDA AKE BAMA ZAKKAR*: 

Ba a bayar ita sai ga wanda yake ya cancanta, sune; Miskinai saboda Hadisin Abdullahi ɗan Abbas wanda muke ta kafa Hujja dashi, wannan itace Fatawar Shaykhul Islam Ibnu Taimiyah a cikin Majmu'ul Fatawa Mujalladi na 25, shafi na 71 zuwa na 78, da kuma ɗalibin shi Ibnul Ƙayyim a cikin bakandamen littafin shi Zaadul Ma'ad a Mujalladi na 2 shafi na 44. 

Duk da haka an samu wasu Malaman sun tafi akan ana iya bayar da ita Zakkar ga dangogin nan guda Takwas waɗanda aka halastar musu karɓar Zakka, sai dai wannan Ra'ayi ne wanda babu wani dalili akan shi, Shaykhul Islam Ibnu Taimiyah yayi raddin wannan Ra’ayi a littafin shi da muka ambata ɗazu.
 
✂️ Yana daga cikin Sunnah a samu wani a bashi ya dinga tara Zakkar a wajen shi, haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) Ya wakilta Sahabi Abu Hurairah – Allah Ya ƙara masa yarda – kamar yadda Imamul Bukhaariy ya fitar a littafin shi mafi inganci bayan Al-Kur'ani. 

 *LOKACIN DA AKE FITAR DA ITA* : 

Ana bayar da wannan Zakka ta Kono kamun Mutane su fita zuwa Sallar Idi, baya halasta ayi jinkirin bayar da ita kamun Sallah ɗin ko kuma gabatar ita sai dai da kwana ɗaya ko biyu wato ana iya fitar da ita kwana daya ko biyu kamun Ranar Sallah, saboda an ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar yana aikata haka, amma idan har Mutum yayi jinkirin bayar da ita bai bayar ba sai da aka dawo bayan Sallah to Zakkar Konon sa batayi ba, kawai dai Sadaka ya bayar irin ta yau da kullum, saboda Hadisin Abdullahi ɗan Abbas da muka kafa Hujjah dashi. 

Allah Ya sa mudace, ya kuma karɓa mana Ibadojin mu, Amin.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)