*MAKARANTAR AZUMI 028* //
📌 ```IDI DA HIKIMAR DA TASA AKA SHAR’ANTA SHI```
Idi guda biyu (2) kaɗai muke dasu a Musulunci: Idin Buɗa-baki baki wanda ake yinshi bayan karewar Watan Ramadan (Ƙaramar Sallah), da kuma Idin Layya bayan cikar kwanaki Goma (10) na watan Zhul-Hijjah (Babbar Sallah).
*HIKIMAR SHAR'ANTA IDI* :
HaÆ™iÆ™a an shar’anta Idi ne; domin Musulmi su bayyanar da farin-ciki da murna, da kuma Godiya ga Allah abisa ni’imar Allah da shiriyar Shi da yayi musu ta hanyar samun daman raya wata alama daga cikin alamomin Musulunci.
*SHAR’ANTA SALLAR IDI* :
Sallar Idi an shar’anta tane da Al-Qur’ani da Sunnah, da kuma haÉ—uwar Malamai magabatan wannan Al’ummar, kuma ita Sunnah ce wacce take ta Wajibi, domin Manzon Allah (SAW) yana yinta a koda yaushe hakama Sahabban Sa, hakama Musulmai suka dinga yinta a bayansu masu mayewa a bayan Magabata.
✂️ Ya zama Wajibi ga Mutane su fita Sallah baki-É—ayan su, domin haÆ™iÆ™a Manzon Allah (SAW) Ya umarci Mata ma su fita domin Sallatar wannan Sallah, sai dai Ya umarci masu fama da lalurar Haila dasu nisanci gurin da ake Sallah wato su fito su saurari Nasihohin da ake yi a wajen Khuduba.
✂️ Lokacin Sallar yana farawa ne da zaran Rana ta É—aga, ya cigaba har zuwa dab da lokacin da zatayi Zawali (wato ta karkata daga tsakiya).
✂️ Abunda yake Sunnah shine a Salla ce ta a fili da yake wajen Gari, amma kuma ya halasta a Salla ce ta a Masallaci idan har akwai wani uzuri da zai hana ayi a wajen Garin; kamar Ruwan Sama ko wani abu makamancin sa.
✍ *ANNASIHA TV*