*HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI ZAKKAR KONO 🍚🍿*
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
*Ma'anar zakkar kono:*
Zakkar kono ita ce zakkar da ake fitarwa a ƙarshen shekara, wato ƙarshen Ramadana, haka kuma ita ake kira zakkar fidda kai.
*Lokacin fitar da zakkar kono:*
Kana iya fitar da ita a cikin azumi tun kwana uku ko biyu kafin a gama azumi har zuwa lokacin da za a tafi sallar idi, kamar yadda Ibn Umar yake yi, haka kuma kamar yadda yake a mazhabarmu ta Malikiyya
Idan ka bari har aka dawo sallar idi, to ta zama sadaka daga cikin sadakoki, amma ba zakatul fitr ba ce, kamar yadda hadisi ya nuna kuma ita ce magana ingantacciya.
*Manufofin shar'anta zakkar kono:*
1. Domin samun tsakaka da laifuka.
2. Domin rage raɗaɗin talauci ga al'umma a ranar sallah.
3. Sannan kuma ita zakkar jiki ce da zuciya
*Nau'in abubuwan da ake fitarwa zakka kono daga gare su:*
Ana fitar da ita ne daga sha'ir, dabino, cukwi, sultu, da nau'o'in abincin da mutane ke ci (kamar shinkafa, masara da sauransu).
*Waɗanda ake fitar wa zakkar kono, kuma ta wajaba a kan:*
Ita zakkar kono wajiba ce a kan kowane musulmi, yaro ko babba, mace ko namiji mai ƴanci ko bawa. Maigida shi ne ke fitarwa ga ƴaƴansa ko bayinsa ko matayensa ko wanda ke ƙarƙashinsa.
*Gwargwadon abin da ake fitarwa:*
Ana fitar da gwargwadon sa'i ɗaya, shi ne mudunnabiyi sallallahu alaihi wa sallama guda huɗu kowane. Wata ruwaya ta ce rabin sa'i in zai fitar daga jar Alkama.
Ina roƙon Allah Ta'ala ya bamu ikon fitarwa, ya gafarta mana laifukanmu, ya amsa mana ibadunmu, ya sa muna cikin ƴantattun bayi a wannan wata mai albarka.
Tsakure daga cikin littafin Bayani kan azumi, wallafar Sheikh Haruna Abubakar Shika Hafizahullah.
*26th Ramadan, 1442H(08/05/2021)*