ALLAAH KA RABAMU DA WANAN HASARA !


ALLAAH KA RABAMU DA WANAN HASARA !

(1). Me yasa har yanzu na kasa rubuta wasiyya dangane da al'amarin jana'iza ta, da wayanda suke bina bashi ko nake binsu, alhalin Annabi yayi umurni da hakan? 

(2). Ga tambaya garemu duka, kowa ya bawa kansa amsa.
***

(3). Wai meyasa idan naje akayi sallar jana'iza bana zuwa makabarta se na koma majalisa na zauna ko kuma kallon film ko wani abu na daban?
***

(4). Ko ko dan bansan girman dutsen bane? ko kuma inada shakku akan kirad'un da Annabi saw yace?
***

(5). Ko me yasa bana tsayawa nayi addu'a akalla na mint 5 akan dan uwa na, amma kuma ni zanso akai awa 1 a nawa?
***

(6). Ko meyasa idan anbirne mahaifina, mahaifiyata, yayana, kanina, yarona, abokina, se na bar kabarinsa ya b'ace min a cikin karamin lokaci, tasanadin rashin zuwa ziyartansu da kula da kabarinsu? 

Muyi nazari me zurfi akan wannan batu kuma mu gyara, meyuwa muma asamu wasu su kula damu bayan wafatinmu.

Yaa Allaah!
ka kashemu a musulunci ka hadamu da bayinka na kwarai.

Yaa Allaah!
Ka amshi ibaadunmu, ka sanyamu cikin yantattun bayinka na wannan wata.

Yaa Allaah!
Ka yayemana dukkan damuwarmu wanda mukasani da wanda bamusani ba.

Yaa Allaah!
ka kawo mana karshen yan ta'adda da ta'addanci na fili dana boye.

Babu abinda nake nufi illa gyara gwargwado, dacewa ta na gurin Allaah, gareshi na dogara, kuma makomata na gareshi.

Assalamu Alaikum w/rahmatLLaah w/barakaatu.

Me kaunarku saboda Allaah! 

*Abuu Ammaar (Al-Od'airy)*

                   28/09/1442/10/05/2021
Post a Comment (0)