💭 MAKO MARKA TANA HANNUNKA ✊🏻
👩👦 MA'ANAR TARBIYYA DA MUHIMANCINTA 👬🏻
1. Ma'anar tarbiyya Wasu malaman tarbiyyar musulunci sun ce : tarbiyya shi ne gina yaro cikakken gini ta bangaren abin da ya shafi akidarsa da ibadarsa da halayansa da hankalinsa da kuma lafiyarsa ta hanyar da ta dace da shari'ar musulunci.
2. MUHIMMANCIN TARBIYYA A MUSULUNCI Tarbiyar yara wajibi ne, Allah yana cewa: ﻳﺎﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺀﺍﻣﻨﻮﺍ ﻗﻮﺍ ﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﻭﺃﻫﻠﻴﻜﻢ ﻧﺎﺭﺍﻭﻗﻮﺩﻫﺎﺍﻟﻨّﺎﺱ ﻭﺍﻟﺤﺠﺎﺭﺓ" Ma’ana (Ya ku wadanda ku ka yi imani ku tseratar da kawunanku da ‘ya’yayanku daga wuta makamashinta shi ne mutane da kuma duwatsu). suratu attaharim aya ta 6 Kuma kowa za’a tambaye shi akan abin da yake kiwo kamar yadda Annabi s.aw. yake cewa: )ﻛﻠﻜﻢ ﺭﺍﻉ ﻭﻛﻠﻜﻢ ﻣﺴﺆﻭﻝ ﻋﻦ ﺭﻋﻴﺘﻪ،..... ﻭﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺭﺍﻋﻴﺔ ﻓﻲ ﺑﻴﺖ ﺑﻌﻠﻬﺎ ﻭﻭﻟﺪﻩ ﻭﻫﻲ ﻣﺴﺆﻭﻟﺔ ﻋﻨﻬﻢ (. Ma’ana : "Kowannenku mai kiwo ne kuma za’a tambaye shi akan abin da yake kiwo, .... mace ma mai kiwo ce a cikin gidan mijinta da dansa kuma za'a tambaye ta akan su. Bukhari da muslim ne su ka rawaito Sharhi Wannan hadisin ya kunshi abubuwa da yawa domin yana nuna cewa duk matar da bata tsaya ta yi tarbiyyar ‘ya’yanta yadda ya kamata ba Allah zai tambaye ta zai kuma mata hisabi akan haka, saboda haka ya wajaba ki yi kokari wajen sa ido akan harkokin ‘ya’yanki . Sannan Annabi (s.a.w.) yana cewa (Babu wani bawa da Allah zai ba shi wani kiwo, ya mutu ranar da zai mutu yana mai algus a cikin wannan kiwon face Allah ya haramta masa aljanna) Bukhari da muslim ne su ka rawaito A wata riwayar ta Bukhari ba zai ji kamshin aljanna ba. don haka za mu fahimci cewa rashin tarbiyyar yara yadda ya kamata yana daga cikin manyan zunubai don haka sai a kula.
✍🏼IBN BASHIR
IBNUL ISLAM
Ibrahim khalil bashir ( SASHA BHAI SINGH )