💭MARKA TANA HANNUNKA✊🏻
👬🏻👨👩👦👦 MATAKIN RAINO DA TARBIYYA 👩👦
Bismillahir Rahmanurrahim ......
Yau za mu duba shin wane ne ya fi hakki a kan tasowar yara da cusu musu ko koyar da su kyakkyawar tarbiyya kyakyawa tsakanin mahaifi da mahaifiya. Kamar dai yadda muka yi ta magana a baya a kan wannan maudu’i na “Raino da Tarbiyya” babu shakka za mu ga cewar abu ne wanda ya shafi dukkan jinsi, wato uwa da uba to amma kuma dole ne a samu wanda nauyin ya fi yawa a kansa. Don haka yau za mu yi kokarin kallon uwa a matakin farko ko kuma jagora a wannan tafiya (Fanni) bisa wasu dalilai kamar hakai: Addini Al’ada Idan muka duba a addinance za mu ga cewar uwa ita ce mataki na farko wajen raino da tarbiyyar ‘ya’ya. Don haka ne ma Hadisin Manzo Allah (SAW) yake cewa a auri mace saboda addininta, Malam Bahaushe kuma yake cewa ka zaba ma ‘ya’yanka uwa ta gari tun kafin ka haife su. Wannan magana na dada nuna mana mahimmancin raino ko kuma a ce yana dada karfafa raino da tarbiyya suna farawa daga uwa kenan. Idan har Allah ya sa uwargida ta haihu lafiya ta gama wankan jego lafiya kuma har Allah ya sa abin da aka haifa na da lafiya, to ba za a bata lokaci ba wurin fara yi masa/mata tarbiyya, dan haka sai uwa ta tsara wani jadawali kamar don kulawa da wasu abubuwa da ya kamata kamar haka: Iya Magana Bayan gida (bahaya) Cin abinci Yin barci da sauran su Iya magana yana da muhummanci kwarai da gasken uwa ta san irin maganganun da za ta rika yi da kuma kalmomin da za ta rika furtawa a gaban yaranta, komai kankantar su domin suna ji kuma suna la’akari da abuwan da take fada. Idan masu kyau ne to za su tashi da su, idan kuma ba masu kyau ba ne haka za su tashi da su, misali iyaye masu wasan zagi haka za ka ga yara kanana na wasan zagin junansu. Uwargida ya kamata ki yi la’akari da lokaci daya, kamata ya yi ki ba yara abinci kar a barsu da yunwa kuma kar a rika cika masu ciki da abinci a’a, a yi sauwa-sauwa. Yin bayan gida: Yana da mahimmanci iyaye su yi kokarin koya wa yara zaman fuwo (ko hawa toilet) da zarar sun kai wani munzali, ba gayu bane a bar yara su kai har tsawon shekaru biyu ko fiye ana sa masu kunzugu (pampers) ba tare da an koya masu yadda za su tsuguna a wurin da ya da ce su yi bayan gida (ba haya) ba. Barci: Haka kuma ya kamata uwa ta yi la’akari da lokacin da yara ya kamata su yi wasa da kuma lokacin da ya kamata su kwanta (yin barci). Yin wannan na sa yara su tashi da sanin lokuttan da ya kamata su tsara ko tafiyar da ayyukansu ma wannan yini (rana).
Ya Allah ka ba mu ikon yin tarbiyya ta yadda ya kamata ga yaran mu, amin.
✍🏼IBRAHIM KHALIL BASHIR ( _IBN ISLAM_ ) MR SBS