*NASIHOHI GA TELOLI MASU ƊINKI*
*1. KIYAYE DOKOKIN ALLAH:*
Wajibi ne ga duk wani mai sana'a ya kiyaye dokokin Allah a cikin sana'arsa. Ya kuma guji sabon Sa, domin hakan yakan jawo albarka mai yawa ga sana'ar.
*2. KIYAYE ALƘAWARI:* Kiyaye alƙawari wajibi ne, domin alƙawari abin tambaya ne. Allah Maɗaukakin Sarki Yace:
*~ {وأوفوا بالعهد إن العهد كان مسئولا } ~*
Ma'ana:
*"Kuma ku cika alƙawari, lallai alƙawari ya kasance abin tambaya."*
*3. KADA KU SANYA ZĀRI WAJEN KARƁAR DUNKUNA:*
Saboda hakan zai sa ku tauye kanku ku kuma tauye iyālanku, kuma manzon Allah (sallalLāhu alaihi wasallam) yace:
*(إن لأهلك عليك حقا ولجسدك عليك حقا ولعينك عليك حقا فأعط كل ذي حق حقه)*
Ma'ana:
*"Lallai iyālanka suna da haƙƙi akanka, kuma jikinka yana da haƙƙi akanka, kuma idānuwanka suna da haƙƙi a kanka, to ka baiwa dukkan mai haƙƙi haƙƙinsa."*
*4. KADA KU FÍFíTA NEMAN DUNIYA AKAN SAMUN FALALAR WATAN RAMADAN:*
Ya tabbata a Hadìsì Manzon Allah (sallalLāhu alaihi wasallam) yace:
*( من أدرك رمضان فخرح فلم يغفر له فأبعده الله )*
Ma'ana:
*"Duk wanda ya riski Ramadan, har ya fita ba'a gafarta masa ba, to Allah ya nisantar dashi."*
*5. KADA NAMIJI YA AUNA MACE KO MACE TA AUNA NAMIJI, IDAN DAI BA MUHARRAMAI BANE:*
Domin Manzon Allah (sallalLāhu alaihi wasallam) yace:
*( لأن يطعن أحدكم بمخيط من حديد خير له من أن يمس امرأة لا تحل له)*
Ma'ana:
*"Wallahi a sōkāwa ɗayan ku masilla ta karfe, yafi alheri gareshi da ya taɓa matar da bata halatta a gareshi ba."*
*6. KADA KU TAIMAKA WAJEN DINKIN MĀTSATTSUN KAYA, KO NA SAKIN TSIRAICI ,KO WADANDA SUKA WUCE IDON SAWU GA MAZA:*
Domin duk lokacin da ka taimaki wani wajen aikata sāɓo, to kaima zaka samu zunubi duk lokacin da aka aikata sāɓon, Allah Madaukakin Sarki Yace:
*~ {ليحملوا أوزارهم كاملة ومن أوزار الذين يضلونهم بغير علم ألا ساء ما يزرون} ~*
Ma'ana:
*"Zasu ɗauki zunubban su cikakku da wani sāshe daga zunubban wadanda suke ɓatarwa ba tare da ilimi ba, ku saurara! Tir da abinda suke ɗauka na zunubbai."*
*7. MAYARWA MAI KAYA SAURAN ABINDA YA RAGE NA KAYAN SA:*
Saboda a lokacinda mai kaya ya bada ɗinki to kayan sa matsayin amana suke ga Tela, don haka wajibi ne ya mayar da amana kamar yadda Allah Ya umurce shi. Allah Yace:
*~ {إن الله يأمركم أن تؤدوا الأمانات إلى أهلها} ~*
Ma'ana:
*"Lallai AllahYana umartar ku akan ku bayar da amana zuwa ga ma'abutanta."*
Allah Ya ƙarfafemu ga bin dōkōkinsa, amin.
Malam Imrana Usman Bukkuyum.