RIKIRA-RIKITAR NAƊIN RAWANIN RAƘUMA
Kimanin mako uku kenan da fitar kafcen Rarumar Maƙiya. Shirin, wanda jarumi Salmanu samɓalin saɓalula ya jagoranta ya fito da ƙarfinsa a ranar murnar sallar kammala azumi da nufin farantawa masoyan jarumin rai, kuma ya samu nasarar yin haka. Sai dai kuma in da gizo ke saƙa shi ne, kasantuwar wannan kafce an haska shi ne a majigin gani da ji na waoyin hannu da kuma bango, an samu saɓani sosai wajen rattabo sahihan bayanan da suka dace game da wannan kafce.
Ba komai ne ya jawo wannan saɓani ba kuwa face ƙarancin fahimtar yadda wannan sabon tsari yake da masu rattabo rahoton suka yi. Kafce dai ba laifi ya yi armashi, musamman ga waɗanda suke ra'ayin kallon jagaliyanci ko barkwanci. Sai dai kuma an yi masa aringizon matsabbai, in da aka yi ta zuzutawa cewa ya ƙwamuso tulin damin hauro daga lalitar 'yan kallo wanda yawansu ya ƙetare hankali. Wannan dalili ne ya sa wasu zaƙaƙuran masu bincike su ma suka zage na su damtsen wajen ganin sun kawo sahihin bayani dangane da wannan kafce. A cikin bayanin nasu, sun bayyana cewa wasu 'yan gani-kashenin jarumin ne kawai ke zuzuta wannan al'amari domin ganin sun yi wa jarumin nasu raɗin rawanin raƙuma masu miƙa wuya sama.
To sai dai kuma hakan be yi wa mabiyan jarumin daɗi ba, inda su ma suka fara mai da martani da cewa hassada ce kawai da bita-da-ƙulli ake yi wa jarumin nasu. A haka dai ake har yanzu inda ake ci gaba da fafatawa yayin da zantuka kuma ke ci gaba da gudana. Ko yaya abun zai kasance daga ƙarshe? Mai-sama shi ya bar wa kansa sani. Sai dai ina ba da shawara ga waɗanda abin ya shafa da su dinga yin nagartaccen bincike kafin su isar da irin wannan bayani kada daga baya azo ana tambayar su suna raba na mujiya.
Na bar ku cikin salama, a ci kaji lafiya.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
08185819176
Haimanraees@gmail.com