KALMOMIN SAKIN AURE :
https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum wa rahamatullah inama mlm fatan alkairi Allah ya. kara wa mlm lafiya.
Dan Allah mlm ina neman karin bayani mijin da yace wa matarsa jeki gidanku babu ruwana dake, shin matar tasaku ko bata saku ba?.
To miji da yace wa matarsa tafi gidanku ba akarkashina kike ba, na biyu kuma yace na hakura dake nagaji.
Iyayena sunce yaban takardata yace shi ba sakina yayi ba. dan Allah mlm meye hukuncin wannan auran?
Saboda gudun fadawa cikin barna. Allah ya saka muku da mafificin alkairi muna matukar amfanuwa.
*AMSA*👇
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Duk Wadannan kalmomin da kika ce ya furta, suna da hatsari kwarai amma ba za'a daukesu kai tsaye amatsayin saki ba, har sai an tambayi mijkn naki shin tsakaninsa da Allah me yake nufi acikin wadannan kalmomin da ya furta din?.
Idan yace saki yake nufi shikenan kin saku. Amma idan yace bai nufi sakinki dasu ba, shikenan baki saku ba. Domin a Musulunci ikon yin saki yana hannun miji ne. Babu wanda ya isa ya sakar masa matarsa sai dai in shi ya saketa da kansa.
Kalmomin saki nau'i biyu ne. Akwai Sareehi akwai wanda ba sareehi ba. Sareehi shine kamar miji yace wa matarsa "Na sakeki" ko "Na sawwake miki" ko "Na rabu dake". Duk wanda ya furta wa matarsa wata kalma daga cikin irin wadannan kalmomin to ta saku. Ko ya yarda ko bai yarda ba.
To akwai kuma kalmomin saki wadanda ba sareehai ba. Misali kamar mutum yace wa matarsa "Tafi gidanku" "Ba ruwana dake" to duk wadannan kalmomin za'a iya nufin saki dasu, kuma zata yiwu a fadesu ba tare da niyyar sakin ba.
Don haka idan har miji ya fadi wata kalma daga jerin irin wannan kalmomin, sai a tambayeshi shin e kake nufi da kalmar nan daka fa'da?".
Wannan ita ce fatawar Imamu Malik da Imamush Shafi'iy (Allah ya jikansu) da kuma mafiya yawan maluman fiqhu.
WALLAHU A'ALAM.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*