FALALAR WATAN RAMADANA



*MAKARANTAR AZUMI 003//* 

📌 ```FALALAR WATAN RAMADANA
``` 
Ramadana Wata ne mai alkhairi da albarka, Allah ya keɓe shi da falaloli masu ɗimbin yawa, waɗanda zasu bayyana kamar haka:

1-   Azumin Watan Ramadana yana cikin ɗaya-ɗayan watannin da yafi kowani Wata falala, Allah Ya ambata cewa wajabta mana azumi da akayi a Watan Ramadana yayi mana haka ne don mu zamo masu tsoron Allah, shi kaɗai cikin watanni yake da irin wannan darajar, Allah Ya saukar da Littafi mafi girma da daraja a cikinsa, Allah Ya sanya daren daraja a cikinsa wato Lailatul Qadri, daren da yafi kowani dare.

2-   Hadisi Ingantacce da Bukhaariy da Muslim suka fitar dashi, daga Sahabi Abu Hurairah, Manzon Allah SAW Ya ce: “ _Idan watan Ramadana yazo, sai a buɗe Ƙofofin Aljannah (a riwayar Muslim yace: sai a buɗe Ƙofofin Rahama), a kulle Ƙofofin Wuta, Kangararru daga cikin Shaiɗanu sai a ɗaure su”._ 

A cikin riwayar Tirmeezhy da Ibnu Khuzaimah yace: “ _idan daren ɗaya ga Watan Ramadana yayi, sai a ɗaure kangararrun Shaiɗanu, a kulle Ƙofofin Wuta, baza’a buɗe kowace Ƙofa ba daga cikin Ƙofofin Wuta, a kuma buɗe Kofofin Aljannah, baza’a kulle kowacce ba daga cikin su._ Sai wani mai kira ya kwalla kira yana cewa: *ina me son aikata alheri yake to ya kusanto, ya matso ga watan aikata* *alkhairi* , *ina me neman aikata sharri to ya taƙaita yayi baya-baya wannan Wata ba watan sharri bane, Allah yana da wasu daga cikin bayin sa da yake ƴantawa a kowani Dare”.*

Waɗannan abubuwan kaɗai sun ishi wannan Wata falala da daraja.

*Twitter* 👇🏿
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09

*Telegram* 👇🏿
https://t.me/AnnasihaTvChannel
Post a Comment (0)