SALLAR TARAWIHI



*MAKARANTAR AZUMI 025* //

📌 ```SALLAR TARAWIHI``` 

 *SHAR'ANCIN TA:* 

1-   Sallar Tarawihi an shar'anta yinta ne a cikin Jama'a saboda Hadisin Nana Aishah (Allah Ya ƙara mata yarda) take cewa: “lallai Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata agare Shi) Ya fita domin yin Sallah a tsakar Dare yayi Sallah a Masallaci, wasu Sahabbai suka zo sukayi Sallah a bayan Annabi, washe-gari Mutane suka ƙara yawa fiyeda Ranar farko, a Dare na uku Mutane suka taru fiyeda Rana ta biyu shima duk Annabi Ya fito ya Sallaci Mutane, suma sukayi Sallah a bayan Shi, da ya kasance a Dare na Huɗu Annabi bai fito ba saboda taruwar da yaga Mutane sun ƙara yi, bayan Annabi ya fito Sallar Asuba sai ya juyo yace musu: “Lallai al'amarin ku bai ɓoyu gare Ni ba, sai dai nayi gudun kada a farlanta muku ita ne, ku kuma kuzo ku gaza daga barin ta” sai Annabi Ya koma ga Allah, al'amarin na nan yadda yake”. [Bukhaariy da Muslim suka riwaito shi.]
 

2-   Bayan barin Annabi duniya ne Khalifah Umar ɗan Khaɗɗab (RA) yazo ya raya wannan Sunnar kamar yadda a cikin Sahihul Bukhaariy, a inda ya samu Mutane a rarrabe kowa yana tashi Sallar a Masallaci, sai yazo ya haɗa su ƙarƙashin Limami guda daya, yin wannan Sallah ba Bidi'a bace, saboda Annabi yayi kuma abunda yasa Annabi ya dena yi gudun kada a wajabta ta akan Mutane, kuma bayan barin Annabi Duniya, tsoron da Annabi yake jima Al'ummar Sa ya kau, saboda dama shi ake ma Wahayi, sai shar'ancin ta ya cigaba da tabbatuwa kamar yadda yake dama a farkon lamari saboda waccar illar ta kau, don haka Sunnah ce tabbatacciya masu inkarin ta suna faɗa ne da Sunnar Annabi kai-tsaye, Allah Ya raba mu da son Zuciya, Amin.


 *ADADIN RAKA'OIN TA* : 

Malamai sunyi saɓani kan yawan Raka’o’in wannan Sallah mai ɗimbin falala, amma maganar da ta dace da Shiriyar Annabi (S.A.W) itace Raka'o'i Takwas ne banda Wutiri saboda Hadisin Nana Aishah (Allah Ya ƙara mata yarda) take cewa: “Annabi ya kasance baya ƙarawa a Ramadana ko ba a Ramadana ba sama da Raka'o’i goma Sha-ɗaya”. 

 *Abunda ya tabbata a Sunnah kenan Raka’o’i goma Sha-ɗaya duk da Sallar Wutiri.* 

Allah Yasa mudace, Amin.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)