SHARAƊIN I’ITIKAFI



*MAKARANTAR AZUMI 024* //

📌 ```SHARAƊIN I’ITIKAFI``` 

1-   Ba’a yin I’itikafi sai a Masallaci saboda faɗar Allah da yace: “ *kada ku sadu da matan ku alhali kuna I’itikafi a cikin Masallatan* ” wannan itace fassara da take daidai kamar yadda yazo daga Sahabi Abdullahi ɗan Abbas (masanin Tafsiri) ana iya duba Sunanul Kubrah ta al-Imamul Baihaqi a mujalladi na 4, kuma Nana Aishah tace: “abunda yake Sunnah ga mai I’itikafi kada ya fito daga masallaci sai saboda buƙatar da take babu makawa gameda ita wato dole ce, kuma bazai je gaida mara lafiya ba, hakanan bazai rungumi matar shi ko yayi Jima’i da ita ba, sannan babu I’itikafi sai a Masallacin da yake ana Sallar Juma’a a cikin shi, kuma abunda yake Sunnah ga wanda zaiyi I’itikafi ya shiga yana da Azumi a bakin shi kamar yadda har-wa-yau Imamul Baihaqi ya riwaito da isnadi ingantacce.

2-   Kuma sannan ana so Masallacin ya kasance ana Sallar Juma’a a cikin shi, saboda kada ya buƙatu don ya fita daga masallacin don zuwa Sallar Juma’a ɗin, saboda dole ne ya fita yin Sallar ta Juma’a, dalili akan haka faɗar Nanah Aisha a cikin riwayar da aka karɓo daga gareta a hadisin da ya gabata: “……………….. *_babu I’itikafi_ _sai a Masallacin_ _da yake ana_ _Sallar Juma’a a_ _cikin shi”.*_ 

3-   To sai dai da haka Ayar tace “Masallatai” ba ana nufin ko wani Masallaci bane koda kuwa wanda ake yin Sallar Juma’a ne a cikin shi, saboda an samu Hadisi ingantacce daga Annabi (SAW) Ya ce: “ *babu I’itikafi sai a Masallatayya guda uku* ”. Sai a Masallacin da Annabi ya gina, Imamud-Ɗahawiy ya fitar da wannan Hadisi da Imamul Baihaqi da isnadi ingantacce daga Sahabi Huzaifah ɗan Yaman – Allah ya ƙara mishi yarda -, ɗan'uwa mai bincike na iya duba sabon bugu na littafin Qiyamu Ramadan da littafin Silsilatul Ahaadethus Saheehah a mujalladi na shida (6) lambar hadisi na 2786 duka na Shaykh Nasiruddenil Albaniy, anan zai ga sauran fatawoyin Sahabbai waɗanda suka dace da abunda muka ambata a sama, kuma dukansu ingantattu ne, sannan a duba littafin Al-Insaaf Fee Ahkamil I’itikaf” na Shaykh Ali Hasan Ali Abdulhamid (Rahimahullah).

4-   Don haka babu I’itikafi a kowani Masallaci indai ba a waɗannan Masallatan guda uku ba;
(i) Masallacin Harami dake Makkah 
(ii) Masallacin Annabi 
(iii) Masallacin Quds).

Don haka ko a Makkah kayi I’itikafi indai ba a Harami kayi ba to I’itikafin ka baiyi ba ɗan’uwa, haka nan ko Madinah ne indai ba a masallacin Annabi kayi ba to baiyi ba. 

Don haka duk wani Masallaci dake garin ku koda ana Sallar Juma’a a cikin shi to ba’a yin I’itikafi a cikin shi, wannan itace maganar Annabi (SAW), Allah ya dawwamar damu akan shiriyar Annabi (SAW), Amin.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)