SHIN ANA IYA YIN SADAKATUL JARIYA GA MAMACI?

*SHIN ANA IYA YIN SADAKATUL JARIYA GA MAMACI?*

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Assalaamu Alaykum warahmatullah!

Malam mutum zai iya yin sadaqatul jariya da sunan wani wanda ya mutu? Da niyar ladar ya rinqa isa makwancin sa har a tashi qiyama? Allah ya saka da mafificin alkhayri.


*AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Ya halasta mai rai yayi wa mamaci sadaka mai gudana kuma mamacin zai amfana da ita har zuwa lokacin da Allah ya kaddara masa. Sannan hakan yana da kyau kwarai da gaske, ba kamar idan mamacin bai samu yayi ma kan sa gatan haka ba. Ga hadisi dangane da haka

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ أَنَّ رَجُلاً قَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّ أُمِّي تُوُفِّيَتْ أَفَيَنْفَعُهَا إِنْ تَصَدَّقْتُ عَنْهَا فَقَالَ: ((نَعَمْ)). قَالَ فَإِنَّ لِي مَخْرَفًا وَإِنِّي أُشْهِدُكَ أَنِّي قَدْ تَصَدَّقْتُ بِهِ عَنْهَا. 

عَنْ عَائِشَةَ أَنَّ امْرَأَةً قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّ أُمِّيَ افْتُلِتَتْ نَفْسُهَا وَلَوْلاَ ذَلِكَ لَتَصَدَّقَتْ وَأَعْطَتْ أَفَيُجْزِئُ أَنْ أَتَصَدَّقَ عَنْهَا فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((نَعَمْ فَتَصَدَّقِي عَنْهَا)). 

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕

Post a Comment (0)