NA GOYA YARONA INA SALLAH DA KASHI A PAMPERS DINSA,YAYA HUKUNCIN SALLATA?


*NA GOYA YARONA INA SALLAH DA KASHI A PAMPERS DINSA,YAYA HUKUNCIN SALLATA?*

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum. Malam Na goya yarona, to pampers din jikinsa da fitsari ko kashi, shin zan iya sallah da shi a bayan ko sai na sauke shi?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salam. Ƴar uwa abin da ya kamata ki riqa lura da shi shi ne, matuqar kashin nan ko fitsarin nan ya fito wajen pampers ɗin, to ki cire masa ki wanke masa, sannan ki goya shi ki yi sallar da shi.
Amma matuqar kashin nan ko fitsarin bai fito wajen pampers din ba, to hukuncinsa kamar hukuncin kashi da fitsarin da ke cikin mutum ne, wato kenan za ki iya goya shi ki yi sallah da shi, saboda akwai mushaqqa idan aka ce kowane lokaci sai kin aje yaron nan idan za ki yi sallah saboda matsalar pampers, wani lokacin ma idan kika aje shi wata qila idan ya sa rigima sallar ma ba za ta yiwu maki ba.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)