*YANA YAWAN CEWA ZAI KASHE KAN SHI, INA TUKI SAI NA BIGE SHI, SHIN ZAN YI KAFFARA?*
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Salamun alaykum ya shykh barka safiya Allah ya qarawa Mallam basira da ikhlasi, Mutum ne ya yake fadawa abokansa da yan' uwansa cewa shifa ya gaji da duniya zai kashe kansa, sai Inna tukin mota kawai yafito mun agabana unexpected sai qaddara tafaru na bugesa ya mutu. Shin Zanyi azumin da kuma Zan biya diyya.
*AMSA*👇
Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Awai abin dubawa da lura a wannan labari. Abin lura na farko, sai an duba yadda hatsarin ya faru da sakamakon da VIO ko yan sanda suka bayar. Wannan sakamako shine zai kubutar da daga laifi ko ya tabbatar da shi a kan ka.
A wajen cimma fitar da wannan sakamako, za'a lura da speed, traffic rules and regulations da kuma lafiya da yananyin ita kan ta motar ka idan ta dace da motar da dokar kasa ta yarje a tuka ta a titinan Najeriya.
Abin lura na biyu, babu ruwan ka ko mu da irin abin da yake tattaunawa ko ambata ma abokan sa, na zai kashe kan sa. Mai yiwuwa, ranar da hatsarin ya faru bai saka ma kan sa mutuwar ba, ma'ana ba da niyya ta riske shi ba, wannan zamu bar shi da Allah ne, ya hukunta shi a kan abinda yake da shi a zuci a daidai lokacin da hatsarin ya faru. Babu wanda ya isa ya yanke masa hukunci sai Allah, toh sai mu kame bakin mu.
Abin lura na uku, duk kisan da ya auku ba da niyya ba, sunan shi kisan kuskure, sakamakon shi, azumi da biyan diyya ga waliyyan mamaci. Don haka a matsayin ka na direba, wannan ya kamata ka shagaltu da shi, babu ruwan ka da abinda ake baka na labarin niyyar sa kafin ya mutu. Abinda ya auku shine ka kashe wani bawan Allah bisa kuskure ba da ganganci ba.
Daga karshe, idan jami'an masana tuki da hanya suka fitar da sakamakon dake nuna cewa, motar ka, asali tana da laifi ko kuma ka zarce speed limit, yanzu kisa ta koma na ganganci. A nan kana da laifi a wurin Allah da gwamnatin kasa. Amma idan sakamako ya tabbatar da kai da mota ba ku da laifi, kuma kana kan yardajjen speed limit, komai lafiya, toh, a nan ya zamo kisan kuskure, baka da laifi a wurin Allah da gwamnati.
Amma idan sakamako ya nuna, shine ya fado maka a lokacin da motar ka da yanayin tafiyar yana kan ka'idar tuki, a nan babu komai a kan ka, na azumi ballantana diyya.
Wallahu ta'ala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*