YAYI KYAUTA GA WANI, WANIN YA RASU, YANZU YAZO YA TAYAR DA KYAUTAR SHI



YAYI KYAUTA GA WANI, WANIN YA RASU, YANZU YAZO YA TAYAR DA KYAUTAR SHI 

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

Slm malam barka da war haka Allah ya taimaki malam ya kara basira tambayata anan shine daya daga cikin ahalin mamaci yayi masa kyauta alokacin da ransa sai bayan ya rasu kuma sai ya karbe abin nan ya matsayin wannan abin yake shin ya halarta abarmasa ko abin ya zama na magada


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Baya halatta a mayar da wannan kyautar ga wanda yayi kyautar, bayan wanda aka yiwa kyautar ya rasu, kuma har zuwa lokacin da ya bar duniya, wannan abin mallakar shi mamacin ne, bai karɓa ba, don haka ko menene a yanzu ya zamo cikin kayan gado, na magada ne.

Amma da yana son tayar da kyautar da sai ya karɓi kyautar sa tun kafin wanda ya baiwa ya mutu, duk da cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya hana hakan, mutum yayi kyauta ya tayar, ta hanyar kwatanta irin wanda ya aikata haka da karen dake amai bayan ya ci ya ƙoshi, sai kuma ya cinye aman shi, 

2193 - «إن مثل الذي يعود في عطيته كمثل الكلب أكل حتى إذا شبع قاء ثم عاد في قيئه فأكله» .
(صحيح) ... [هـ] عن أبي هريرة. الصحيحة 1699: حم.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)