MENENE ADADIN DIYYAR RAI?
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin alkairi ya shirya xuriya ya ƙara daukaka da sutura Ameen. Malam menene adadin diyar Rai?
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.
Adadin diyyar Rai a musulunci shine Raƙuma Ɗari. Hadisi yazo a Sunanun An-Nasa'iyy cewa diyyar Rai na mumini (mace ko namiji) Raƙumi Ɗari (100) ne, amma ga waɗanda basu da Raƙuma, Dinari Dubu (1000) ne
رواه النسائي عن أبي بكر بن محمد بن عمرو بن حَزم عن أبيه عن جده رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم قد كتب كتابًا إلى أهل اليمن جـــاء فيه: «أَنَّ مَنِ اعتَبَطَ مُؤمِنًا قَتلًا عن بَيِّنةٍ فإنه قَوَد إلا أَن يَرضى أَولِياءُ المَقتُولِ، وأَنَّ في النَّفسِ الدِّيةَ؛ مِائةً مِنَ الإبِلِ -إلى أن قال صلى الله عليه وآله وسلم- وأَنَّ الرَّجُلَ يُقتَلُ بالمَرأَةِ، وعلى أَهلِ الذَّهَبِ أَلفَ دِينارٍ».
Yazo a Sunan na Abi Dawud cewa diyyar Rai a zamanin Annabi Dinari Ɗari Takwas (800) ne, ko Dirhami Dubu Takwas (8000). Amma a zamanin halifancin Amirul Muminin Umar sai yayi huɗuba, yace haƙiƙa Raƙuma sun yi tsada, saboda haka ya mayar da diyyar Rai Dinari dubu (1000) a madadin Ɗari Takwas, Azurfa kuwa Dubu sha Biyu (12,000), ko Shanu Ɗari Biyu, ko ƙananan dabbobi (Awaki da Tumaki), Dubu Biyu (2000)
وروى أبو داود أيضًا من حديث عَمرِو بنِ شُعَيبٍ عَن أَبِيه عن جَدِّهِ قال: "كانت قِيمةُ الدِّيةِ على عَهدِ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وآله وسلم ثَمانِمائة دِينارٍ أو ثَمانِيةَ آلافِ دِرهَمٍ.. قال: فكانَ ذلكَ كذلكَ حتى استُخلِفَ عُمَرُ رَحِمَه اللهُ، فقامَ خَطِيبًا فقال: أَلا إنَّ الإبِلَ قد غَلَت. قال: ففَرَضَها عُمَرُ على أَهلِ الذَّهَبِ أَلفَ دِينارٍ، وعلى أَهلِ الوَرِقِ اثنَي عَشَرَ أَلفًا، وعلى أَهلِ البَقَرِ مائَتَي بَقَرةٍ، وعلى أَهلِ الشَّاءِ أَلفَي شاةٍ، وعلى أَهلِ الحُلَلِ مِائَتَي حُلَّةٍ..".
A yau 4/10/2020, Dinari ɗaya yana daidai da *4.25gm* na *22k na Gold* (zinari). A yau kuma farashin irin wannan zinari, a Kaduna, Nigeria, Naira Dubu Ashirin da Tara ( *₦29,000:00*). Ke nan adadin kuɗin diyyar rai, a wannan yanayi, a kuɗin ƙasar mu Nigeria, a yau zai kama, *Naira Miliyan Ɗari da Ashirin da Uku, da Dubu Ɗari Biyu da Hamsin* ga yadda yake
1000dinarix4.25gmx₦29000=
*₦123,250,000:00k*
Amma wannan adadi na kuɗi na canjawa daga lokaci zuwa lokaci, ko ya rage ko ya ƙaru, ya danganta da tashi ko saukan farashin dalar Amurka ko shi kan shi Zinarin.
Abin da adadin shi baya canjawa sune, adadin Raƙuma, Awaki da Tumaki, Dinari, Dirhami, Azurfa ko Zinari, sai dai ƙimar su ta canja.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa.*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*