YA HUKUNCIN MASUYIN GABA DA JUNA,DA KUMA YIN WASIYA DA HAKAN
*TAMBAYA*❓
Assalamu allaikum
.
Malam ya kake ya Gida ya hakuri da irin mu
Mallam don Allah in son ka fahintar dani akwai wani Abu ne da yashige min duhu don ALLAH malam mene ne hukuncin Gaba sakanin musulmi da musulmi har yakai yakawo babu ko sallama Tsakanin su shin koda iyayenka neh da wasu suke irin wannan gaban zaka iyayin biyayya agare su duk dace malamai suna CE Babu biyayya ga dan Adam wajen sabawa ALLAH
Shin hardaya daga cikin su ya furta wannan kalman kamar haka
Koda bayan Ransa neh bai yarda dan gidan makabcin sa ya auri yarsa ba shin kana ganin wannan wasiyar tayi ke nan malam ALLAH yakaramaka lapiya da imani malam
Jaxakallahu fill jannah
*AMSA*👇
Wa,alikumussalam da farkodai yakamata a bincika meya hadasu, sekuma ayi qoqarin dai-daita su, "domin an fasa sauqar da lailatul qadari sakamakon fada da wasu daga Cikin sahabbai sukayi, aka daga ranan zuwan ta izuwa sauran kwanakin" hakanan Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya haramta musulmai suyi kwana uku batare da sunyi magana da juna ba, wato abinda ya shafi fada, gaskiya akan wannan akwai Uguba babba, yakamata ku musu nasiha ko kusa a musu....
.Abin da ya shafi wasici dayayi kuma wannan bazatayi Amfani ba, matuqar Sabon ALLAH ne domin ba'ayiwa wani da'a cikin sabon ALLAH, da ace su dayan gidan sunada mummunan dabia ne, tofa baza'a hanaka bin wannan Umarnin ba, amma idan kace zaka Aura daga baya, dan samun maslah wannan ba matsala in sha ALLAH, Domin shi wasiyya anayi akan dayan biyu ko wasiya da hakuri ko da gaskiya... Kaman yada Suratul asar ta nuna
.
Shiyasa Imam shafi'ie yace "idan da ALLAH be sauqar da wata hujja akan halittun sa ba, se wannan surar (suratul asir) da ta ishesu" _usulus salasa_
.
A wani waje yace "lalle mutane ko mafiyya yawan su, basa ta dabburin waccar" suratul asar....
.
Tabbas damuna tunani akan su, da bazamu fada cikin halaka ba, ayata biyu cikin surar ALLAH yace " lalle mutum yana cikin asara.
2- se wadanda sukayi imani, suka aikata aiki me kyau, sukayi wasiyya da gaskiya, kuma sukayi wasiya da hakuri!!. ( wato cikin Yima ALLAH biyayya)
.
duk wanda yayi wasici da 6arna baza'a aikata ba!!
.
SULHU SHIYAFI ALHERI, KUBI HANYAN GYARA TIN KAFIN MUTUWA TAZOO..
.
Wallahu a,alam
Muhammad Auwal Hussain (Abu-Ja'afar)
Zaku iya samu wannan group na Facebook da na telegram ta wannan hanyar
TELEGRAM👇🏻
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177