ALLAH KA SA MU YI KYAKYAWAN ƘARSHE


Da NEPA suka ɗauke wuta sai na tashi na rufe ƙofan ɗakina sa'annan na kashe switch na wuta tsoron kar su kawo ina barci, sa'annan na zauna na gabatar da adduo'i da ya sauwaƙa mun na barci, bayan na gama sai na kwanta.

Duk abunda nakeyi ɗinnan ido na a rufe yake, ina kwanciya sai na buɗe ido na kawai sai naga baƙin duhu, kawai sai na tuna kabari da kuma yadda duhun gurin zai kasance, na tuna ya tabbata a kimiyance da ta hanyan wahayi cewa zan kasance ina sane da halin da nake ciki tun daga mutuwa ta zuwa a sani a kabari cikin wannan rami.

Na tuna yanda zan kasance a ciki, ni kaɗai, goshi na kabari ƙeyana kabari ƙirjina da cikina kabari bayana kabari kan yatsun ƙafana kabari dunduniya na kabari, ga duhu ga kaɗaici gashi hadisai ingantattu sun tabbatar kowa ya shiga kabari sai ta matse shi sai dai aikin sa ya kuɓutar dashi, gashi ba wajen gudu. Innalillahi wa inna ilaihi ra'ji'un.

A kwai abun mamaki a wajen duk wanda ya yarda a kwai wannan a gaban sa amma bai sa shi gyara aikin sa ba.

Don haka Annabin Rahama s.a.w. ya umurce mu da gyara sallolin mu da karanta Suratul Mulk da daddare don sune za su zama abokan zaman mu a kabari yayin da muke cikin kaɗaici.

Allah nake roƙo ya lulluɓe mu da Rahaman sa ya azurta mu da kyakkyawan ƙarshe ya azurta mu da kyakkyawan makoma, ya kare mu daga duk wata nau'i na azaba a cikin kabarin mu👏🏾
Post a Comment (0)