MACE ZA TA IYA SHAYARWA A GABAN MUHARRAMINTA?



Tambaya
:
Shin ko ya halatta mace ta shayar da ɗanta nono a gaban muharramanta? Sannan ina ne ya ke iya zama tsiraicin mace a wajen muharramanta?
:
Amsa:
:
Dangane da hukuncin mace ta fito da nononta waje a gaban muharramanta don ta shayar da ɗanta, an samu maganganu kamar guda uku na Malamai a game da saɓanin da sukayi dangane da cewa ina ne iyakar tsiraicin 'ya mace a gaban muharramanta kamar:
:
Ɗanta
Babanta
Ɗan Mijinta
Ɗan'uwanta
Ɗan kaninta
Ɗan yayanta
:
(1)-Ƙauli na farko shi ne, abinda Mazhabin Malikiyya da kuma Hanabila suka tafi a kansa cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta ya game dukkan jikinta ne amma banda fuskarta, annayenta, kafafuwanta, da kuma gashin kanta. Amma ba ya halatta a gareta ta bayyanar da kirjinta ko nonuwanta a gabansu. Danhaka haramun ne muharraminta ya ga kirjinta ko nonuwanta, ko da kuwa mahaifinta ne shi, sannan kuma ko da ba da nufin sha'awa ko jin daɗi ya kallaba.
:
(2)-Ƙauli na biyu kuma shi ne, Mazhabin Hanafiyya sun tafi a kan cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin cibiyarta zuwa guiwowinta da cikinta da kuma bayanta. Danhaka ya halatta ya ga dukkan sauran jikinta in banda waɗancan wuraren, amma sukace da sharaɗin ya kasance an aminta da cewa babu wata fitina da a ke zaton kallon zai iya haifarwa, sannan kuma ya zama ba kallo ba ne ze yi mata irin na sha'awa, idan kuwa kallon sha'awa ne ze yi mata ko kuma ita za ta ji sha'awa ko dadi a dalilin hakan, to haramun ne ya ga ni.
:
(3)-Ƙauli na uku shi ne abin da Mazhabin Shafi'iyya suka tafi a kan cewa tsiraicin Mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin cibiyarta zuwa guiwowinta kaɗai, sukace ya halatta Muharraminta ya iya ganin fuskarta, hannayenta, kafafuwanta, gashin kanta, kirjinta, nonuwanta, cikinta, da kuma bayanta. Shin muharramin nan Ɗan'uwanta ne shaƙiƙi na jini ko kuma Ɗan'uwanta ne da suka sha nono tare, duk hukuncinsu ɗaya ne.
:
To amma sai dai maganar da mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da ita itace, Ƙaulin da Mazhabin MALIKIYYA suka tafi a kansa na cewa dukkan jikin mace tsiraici ne, sai dai ya halatta muharramanta su iya ganinta a yanayin da a bisa al'ada a ke iya ganin wasu wurare sukan bayyana a jikin mace idan tana yin wasu aikace-aikace irin na cikin gida.

Wato kamar zira'in hannayenta, wuyanta, gashin kanta, da kuma Ƙafafuwanta zuwa guiwarta.
:
Amma dangane da hukuncin tsiraicin Mace a gaban 'yan'uwanta Mata ko da kuwa waɗannan matan 'yan'uwanta ne na jini, wasu daga cikin Malamai sukace tsiraicin mace a gaban 'yan'uwanta mata dai dai yake da hukuncin tsiraicinta a gaban muharramanta, danhaka sukace ba ya0 halatta mace ta bayyana tsiraicinta kamar cinyoyinta da nonuwanta da cikinta zuwa cibiyara a gaban wasu Matan, sai dai in da wata larura mai ƙarfi, amma sai dai wasu Malaman sun tafi ne a kan cewa hukuncin tsiraicin Mace a gaban 'yan'uwanta mata dai dai yake da hukuncin tsiraicin namiji a gaban ɗan'uwansa namiji, wato daga cibiya zuwa guiwa, to haka suma Mata a tsakaninsu daga cibiya zuwa guiwa,
:
Daga ƙarshe idan mukayi duba a kan maganganun da Malamai sukayi za muga cewa magana mafi inganci itace haramun ne Mace ta fito da nonuwanta fili a gaban muharramanta dan ta shayar da jariri. danhaka ya zama wajibi a kanta ta san duk yadda za ta yi ta suturce nonuwanta a lokacin da ta ke shayar da Ɗanta.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)