BUDURWA MAI TSADA



BUDURWA Me Tsada,ko da KuÉ—inka Sai da Rabonka Alaji............

👉Ina ta Fito neman Ilimi ina zata Neman Ilimi,Me kula da Ibadah ce Gwargwado,da qoqarin Aiki da Ilimin natá.

👉Da ka ganta ta fito waje wuri me mahimmanci zata tafi,ko kuma Aikenta akayi,ko wani Uziri.

👉Da Wuya kaga tana kula Samari Sai wanda ya isa ma'ana ya biyo ta Hanyar Girmamawa da Darajawa,sannan shima kansa ya san me yake yi a Rayuwa Nitsatstse ne,kuma yawanci sai Iyaye ma sun Yarje sannan zata Saurare shima ɗin.

👉Ko a cikin Gidansu za'a sameta me Girmama Yayyunta da Iyayen ta ce,balle a waje tana mutunta Al'umma,Jajirtacciya wurin Taimakawa Mama da Aikin Gida,kuma Gwana ce wurin Tsafta idan bata Gidan sai anyi kewarta musamman ma Mama,sannan me Haquri ce da Juriya kan Akwai da Babu.

👉Bata da Hayaniya balle a sameta tana Dambe da wasu ko wata Hayaniya akan Titi,Hasalima idan taga anayi Raɓewa take ta wuce abinta musamman idan Maza ke Hayaniyar,kuma bata Yawon Shiririta da Qawaye,Qawayenta ma kusan duk Masu Hankali ne.

👉Bata da dogon Buri tana da Iymanin Rabonta bazai wuce taba,kuma bata da Kwaɗayin abin Hannun Samari,sannan ba Burinta ne tara Samari ba,burinta shine Allah ya bata Miji na Gari me Qaunarta domin Allah.

👉Idan tayi Furuci cikin kalmominta cike suke da sanin ya Kamata,babu Tozarci ko Raini balle Ballagazanci a cikinsu.

👉Idan ka ganta tana Tafiya a Hanya bata karairaya,balle Turo Qirji da Rausaya,babu ciye-ciye ko shewa da sauransu,a Nutse take Tafiya kuma kusan ko yaushe tafi zaɓar Can gefen Hanya,sannan Sutturar jikinta ba me nuna tsaraicinta bace.

👉A Rayuwarta ta Yarda Allah shine Ubangijinta,kuma duk abin daya risketa wurinSA zata kai kukanta,bata yarda taje wurin Wani ko wata domin yayi mata wani Tsubbu ba kan wata matsala,Sannan me Riqe Amanar Kanta ce iya wuya Jikinta Mallakin Mijin daya Aureta ne,ta Yarda duk wanda ya neme ta da Alfasha ko ɗan waye ko wanene ta Rabu dashi kuma ta fita daga Harkarsa.

Allah ya Inganta Tarbiyyar Ƴaƴan mu.
Ameen.
Post a Comment (0)