CIWON SUGAR (DIABETES)
Rubutawa: Muhammad Ibrahim Bawa
Ciwon suga (Diabetes) ciwo ne wanda suga (Glucose) yake yawa a cikin jinin jikin mutum lokacin jikin mutum ya kasa sarrafa dukkanin sinadarin da suga (Glucose) ke bukata sai suga ya yi yawa a jiki yawansa na faruwane sabida jikin baya amfani da sinadarin da ke rage yawan suga a jiki (Insulin) ko kuma jikin baya samar da sinadarin da ke rage yawan suga isasshe.
Idan babu sinadarin da ke rage yawan suga a jikin dan Adam (Insulin) suga (Glucose) zai samu gurin taruwa a jikin dan Adam har yayi illa ga lafiyar jikin dan Adam.
Ciwon suga na daya daga cikin cututtuka dake damun al'ummar duniya alkaluma ya nuna a kalla sama da mutum miliyan hudune ke dauke da cutar a duniya dayawansu basu san suna duke da cutar ba bincike ya nuna ciwon ne sanadiyar mutuwar masu dauke da wannan cuta a cikin kowane second goma.
Rabe raben ciwon suga
Ciwon suga ya rabu izuwa gida biyu:
1- Nau'in ciwon suga na daya insulin dependent wannan na faruwane lokacin da jikin dan Adam ya daina samar da sinadarin dake rage yawan suga a jikin mutum (Insuline) ta dalilin haka sai suga ya taru a cikin jini kimanin kashi goma cikin dari na masu wannan cuta ke dauke da wannan nau'i wannan nau'i na ciwon yafi yawan kama kananan yara da samari amma wani lokaci yakan shafi mutane a kowane shekara masu wannan nau'i na cuta suna bukatar sinadarin dake rage suga a jikinsu (insulin) domin ya dauke suga (Glucose) dake cikin jini zuwa cikin kananan halittu da suka yi ganin jikin dan Adam (Cells) domin samun kuzari a garesu da cigaban rayuwarsu.
2- Nau'in ciwon suga na biyu non insulin dependent wanan ciwon na faruwane lokacin da jikin dan Adam baya samun isasshen sinadarin rage suga (Insulin) ko sinadarin ya zamanto baya aiki kashi casa'in cikin dari na masu wannan cuta ke dauke da ita masu shekaru sama da arba'in ko tsoffi su sukafi kamuw da wannan cuta.
Daga lokacin da aka samu mutum da daya cikin wannan nau'i matukar bai tsananta a jikinsa ba ta inda baya iya gane cewa yana cikin hayyacinsa a bi daya daga cikin wadannan hanyoyi insha Allah zai dawo cikin hayyacinsa amma in ciwon ya tsananta sai ayi sauri a kaishi asibiti dan a duba shiga hanyoyin:
a- A samu tuffa (Apple) a markada a baiwa mutun ya sha ruwan
b- A bawa mara lafiyar dabino guda biyu da ruwa ya sha
Dalilain kamuwa d ciwon suga
1- Gado: Idan aka samu wani cikin iyaye ko dangi da k dauke da ciwon suga nau'i na biyu (Non insulin dependent) ana iya kamuwa da cutar.
2- Nauyin jiki: Lutantaka
3- Kuncin rayuwa: Wannan ma yana taimakawa wajen saurin kamuwa da cutar sai dai ba a daukar wannan a matsayin yanayin kamuwa da cutar lokaci guda.
4- Tsufa ko matsakaicin shekaru:
Alamomin kamuwa da ciwon suga
1- Ramewa babu wani dalili
2- Matsalar rauni wajen gani (Raguwar karfin ido)
3- Bushewar baki da jin kishin ruwa mai tsanani bana al''adabi wanda yake yawan maimaituwa
4- Yawan jin fitsari sau dayawa a rana musamman cikin dare
5- Yawan soshe soshe a gabobin jiki
6- Gajiya a yawancin lokuta
Hanyoyin da za a bi wajen kaucewa kamuwa da wannan cuta
Akwai hanyoyi dayawa da za a bi don kaucewa wannan cuta kadan daga ciki sun hada da:
1- Yawan motsa jiki, binciken masana ya nuna motsa jiki yakan kona kasa saba'in bisa dari na kitse dake taruwa a jikin dan Adam wanda kitse idan ya yi yawa yana matukar taka rawa wajen kawo wannan cuta.
2- Rage cin abincin dake dauke da carbohydrate, idan har cinma ya zama dole yana da kayau a hada da kayan ganyayyaki kamarsu latas, cabbage, carrot, cucumber da sauransu.
3- Kada aci abinci mai nauyi a kwanta a take
4- Rage cin jan nama musamman mai kitse, idan son samune afi yin amfani da kayan ciki musamman hanta, sannan kifi.
5- Rage yawan shan madara mai maiko a rika sirkawa da ruwan bunu lokaci zuwa lokaci.
6- Yawan amfani da kayan itace irinsu lemu, kankana abarba, tufa da sauransu.
7- Yawaitar iyartar likitoci da zarar kaji wani alama na wannan cutar idan san samune mutum ya samu abin gwajin suga (Glucometre) ko kuma ka ware wasu lokuta ana gwada level ne suga ka normal level shine 4 zuwa 5, 6, 7 ne ya danganta da karfin jinin jikin mutum. Amma idan yakai 8 zuwa sama da akwai mtsala sannan idan yayi kasa da 4 yana shafar ido kaga mutum ya makance ko kuma baya gani sosai (raunin ganin ido).
8- Kiyaye lokacin cin abinci akalla mutum ya rika cin abinci sau uku a lokacin daya saba.
9- Gujewa cin abinci sanda aka koshin domin hakan na cutar d jikin dan Adam.
10- Gujewa cin abubuwan da suka shafi kayan zaki
11- Gujewa shan taba
Dagacikin tsiran dake da amfani wajen magance ciwon suga
1- Albasa da kabeji: A hadasu guri guda ana ci kullun ko a markadesu ana shan ruwan.
2- Tafarnuwa da zuma: A sami tafarnuwa guda hudu a bare a sanya a cikin wani roba ko wani abu mai murfi a zuba zuma mai kyau ya rufe tafarnuwan a sanya a cikin fridge ko wani abu abarsu su jiku na sati daya sai a dauko ana sha har na tsawon wata guda kafin a ci komai.
3- Kubewa (Okra) a yayyanka shi a sanya a wani abu a jika shi da ruwa ya kwana ingari ya waye a tsiyaye rowan ana sha kafin aci komai da safe.
4- Garahuni (Bitter melon) wannan yana matukar amfani wajen magance ciwon suga a nau'i na farko da na ambata a baya a markadeshi a rika shan ruwan.
5- Ganyen bay (bay leaves) wannan yana taimakawa wajen magance ciwon suga nau'i na biyu dafawa akeyi ana sha kamar shayi.
6- Garin cinnamon da garin raihan (doddoys) a hadesu gu guda a dafa ana shad a safe kafin aci komai.
7- Ginseng bincike na masana ya tabbatar da cewa ganyen ginseng na tasiri wajen rage suga dake jikin mutum.
8- Citta: ya tabbata cewa yana rage suga dake jini.
9- Zaitun: binciken masana ya nuna cewa ganyen zaitun na daga cikin ganye mafi muhimmanci wajen warkar da ciwon suga ana dafa ganyen ko garin zaitun a sha da zuma da safe kafin aci komai sai kuma da daddare.
10- Garin habbatussauda da manta: garin habba da manta na taimakawa wajen magance matsalar ciwon suga za a rika amfani da shi sau uku a rana har na tsawon wata uku.
11- Ganyen darbejiya: ganyene mai matukar amfani yana taimakawa wajen magancen matsalar ciwon suga.
12- Green tea da kurkum za a hadesu guri guda a dafa a na sha.
Maganin ciwon suga
1- A samo ganyen doddoya a hada dana shuwaka a cakudasu guri guda sai a anya tafarnuwar da ruwa a ciki a rika sha karamin kofi sau uku a rana.
2- A samo man zaitun a hada da madara da lemun tsami a rika sha da safe kafin a ci komai sai kuma daddare, bayan nan sai a samu ganyen zaitun a rika tafasawa a na sha tare da zuwa.
3- A samo habbatussauda busasshen kabeji, bawon ruman, mur hiltit yawan su ya zama daya a hadasu guri guda a rinka cin karamin cokali guda kafin a ci komai da kuma daddare.
4- A samo garin habbaturrashod, habbatussauda a garin bawon rumman, mur a hadasu guri guda a sanya cikin wani abu mai murfi a juye a gun sanyi ko cikin fridge a rika cin karamin cokali kafin a ci komai da minti 30.
5- A samo tuffa, ayaba, kabeji, kiwi a hadasu guri guda da ruwa a markade a blander ko wani abu a rika shan ruwan na tsawon wata shida insha Allahu za a warke.
Tasririn hijama wajen warkar da ciwon suga
Hijama hanyace na warkar da cutuka manya da kanana da izinin Allah an samo hijama ne daga الحجم wato zuka ana amfani da hijama wajen zuko cuta daga cikin jinin jikin mutum Manzon Allah SAW yayi kaho ya kuma sanyashi cikin abunda ake samun lafiya tattare dashi.
Hijama nada matukar tasiri wajen magance matsalar ciwon suga ga mai fama da ciwon suga kowane iri sai amai hijama sau uku cikin wata uku kowane wata sau daya za a yi hijamar a lambobi kamar haka 1, 55, 6, 78, 22, 23, 24, 25, 120, 49 in sha Allah za a samu waraka amma a kula wajen yin hijmar kada tsagun ya wuce guda uku bayan an gama kuma a samu zuma ko habbatussauda ana shafewa a gurin da aka yi hijaman na tsawon kwana uku.
Ga mai neman magani na ciwon suga ko wsuma maguna na wasu laluran daban ko kuma yake bukatar amai hijima domin samun waraka da yardar Allah sai ya emeni ta wadannan hanyoyi
Lambar waya:+2347039392072
Gmail:muhammadibrahimbawa7@gmail .com
Adreshi135/14 idi mai barkono street gidan malam Ibrahim Bawa Mai Shinkafa
Muhammad Ibrahim Bawa Mai Shinkafa