WA YA DACE NA AURA?



*👫WA YA DACE NA AURA?🌹*

Mafi girman kuskure da mutum zai yi a rayuwarsa shi ne ya kuskure wajen samun aboki/abokiyar rayuwa mai nagarta, wannan wani babban al'amari ne da zai shafi rayuwar mutum da zuriyyarsa.

Samun natsuwa na daga cikin manyan manufofin shari'a na yin aure, daga lokacin da aka rasa natsuwa, to hakika an rasa wani jigo babba a zamantakewar aure.

Shi ya sa da annabi (ﷺ) yana bayanin sifar mutumin da ya cancanta a ba shi aure, sai ya ce *mutum mai addini da kyawawan halaye.*

Mutane da yawa kansu ya kan rikice game da mutumin da za a iya siffanta shi da waďannan manyan siffofi guda biyu. Waďansu tunaninsu shi ne mutum mai tarin ilimin addini shi ne ake nufi da ma'abocin addini, sam-sam bā haka abin yake ba.

These qualities are independent of one another, zā ka iya samun mutum mai addini wanda ba shi da kyawawan ďabi'u, kamar yadda za ka iya samun mutum mai kyawawan ďabi'u amma ya rasa addini. Babbar naqasa ce a rasa mutum da ďayan waďannan abubuwa guda biyu, kuma za a yi nadama idan aka bayar da aure ga mutumin da ya rasa duka ko ďayan waďannan halaye. 

— *Mutum mai addini* shi ne wanda yake da ilimin addinin musulunci ko yake 'kokarin neman ilimin, yana da taka tsan-tsan wajen kiyaye tsakaninsa da Mahaliccinsa, ba za ka samu yana wasa da sallah ba, yana azumi da sadaka kuma yana kamewa daga aikata manyan zunubai. Ba za ka ta6a samun mai irin wannan halayya ba sai a cikin musulmai.

—Shi kuwa mutum *mai kyawawan ďabi'u* shi ne wanda yake da Kyakkyawar mu'amala tsakaninsa da mutane; yana da sakin fuska kuma bā ya cutar da mutane, yana da hakuri, bā ya ha'inci, za ka samu ba shi da matsala tsakaninsa da mutane. Bā a cikin musulmai kaďai ba, har a cikin kafirai ana iya samun irin waďannan mutane.

Namiji ko macen da ke da waďannan siffofi guda biyu, kuma yana da lafiya da sana'ar da zai iya ciyar da iyali, to haqiqa idan an ba shi aure ba za a yi nadama ba.

Amma sau dayawa zā ka samu mutum yana da addini, amma idan ya rasa kyawawan ďabi'u, sai a samu matsaloli masu yawa a zamantakewa. Mai yiyuwa ba ya kyautata mu'amalarsa da iyalansa da sauran mutane, be iya nuna soyayya da tausasawa ba, ko yana cutar da iyalansa.

Za ka samu wani namijin ba shi matsala da iyalansa, 'yan uwansa da sauran mutane, ana yabonsa ta fuskar mu'amala, amma sai ka samu mazinaci ne, ko yana wasa da sallah, be iya karatun alqur'ani ba kuma ba ya 'kokarin neman saninsa, bā yā kishin iyalinsa idan ya ga suna aikata abin da Allah Ya hana, be damu da ďora iyalinsa a kan al'amuran lahira ba. Ko mace mai kyautata wa mijinta, amma sam ba ta damu da sallah a kan lokaci ba, ita ce sauraron wake-wake da kallace-kallacen fina-finai barkatai.

*🌀Miji nagari* shi ne wanda yake tsare tsakaninsa da Mahaliccinsa, kuma yake kyakkyawar mu'amala da mutane, yana amfanar da mutane kuma ba ya cutar da kowa, mai 'kokarin kiyaye iyalansa daga jin kunya a duniya da kare su daga shiga wuta a ranar alqiyamah.

Madallah ga wanda ya dace da waďannan siffofi!

Barka ga wacce ta dace da namiji mai addini da kyawawan halaye! 

Jinjina ga wacce ta kawar da idanunta daga 'kyale-kyalen duniya ta bi za6in da Mαnzon Allαн(ﷺ) ya yi mata. 

Mu natsu mu yi wa yaranmu zabin uba/uwa masu addini da kyawawan halaye, sai a samu zuriyya mai albarka, kuma a samu farin ciki da natsuwa a zamantakewa. Idan an ga kuskure a rubutuna don Allah a ankarar da ni.

Ina rokon Allah Ya sanya mu cikin bayinSa masu addini da kyawawan ďabi'u, kuma Ya datar da mu da abokan rayuwa masu nagarta 👏🏾
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*08166650256.*
*15-06-2021.*
Post a Comment (0)