HUKUNCIN AIKI A HOTEL DIN DA AKE SIYAR DA GIYA



HUKUNCIN AIKI A HOTEL DIN DA AKE SIYAR DA GIYA

*Tambaya*
Assalamu alaikum ya Sheikh inada tambaya
Hukuncin yin aiki a matsayin accountant ko receptionist a hotel da suke da sashin sayar da giya aciki da kuma ya halatta mutum yayi aiki da Private pension fund? Na gode

*Amsa*
Wa'alaykumussalam
Baya halatta ayi aiki a irin wannan hotel din ba don daga cikin wadan da manzon Allah ya ce Allah ya la'ance su akwai "... Mai saida giya da mai cin kudin giya" kamar yadda ya tabbata cikin hadisin Abdullahi dan Umar da Anas dan Malik wanda Abu Dauda 3674, Ibn Maaja 3380, da Tirmizy 1295 Suka ruwaito.
Sannan kuma yin irin wannan aikin taimakawa ne wajen barna da baiwa mai barnar mafaka wanda shima manzon Allah yace Allah ya tsinewa mai ba mabarnaci mafaka a cikin hadisin Aliyu bn Abi-Dalib wanda Muslim ya ruwaito 1978.

 Maganar aiki a pension board ko Fund kuwa a tura tambatar zuwa ga Dr. Jamil Zarewa ko Dr. Bashir Aliyu Umar Allah ya kara tsare mana su da mu baki daya.

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

4/02/2021

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)