HUKUNCIN HUDA HANCI DA SAKA ZOBE KO SARKA A KAFA



HUKUNCIN HUDA HANCI DA SAKA ZOBE KO SARKA A KAFA

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu

Malam don Allah yaya kwalliya da hudan hanci,gyaran gira, zoben kafa da sarkan kafa suke amusulunci? Nagode.
Allah saka da alkhairi

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Malamai sunce hujin hanci da hujin kunne duk ya halatta ga Matayen musulmai.
Domin kuwa matan Sahabban Manzon Allah (saww) sun kasance sunayi kuma Annabi (saww) bai hanasu ba.
Acikin FATHUL-BAREE juzu'i na 10 shafi na 407-408, Al-Imam Ibnu Hajrin ya kawo wani hadisi wanda Tabarany ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Ya lissafta abubuwa bakwai sunnah ne ga dukl wata 'ya-mace. Daga ciki akwai hudar hanci da hudar kunne.
Amma malamai sunce wajibi ne kowacce mace ta tabbatar da cewa ruwa yana ratsawa cikin wannan hujin yayin da tazo yin wankan haila ko janabah.
Dangane da sarkar Qafa da zoben Qafa kuwa, rashin sanyasu shine mafi alkhairi.
Domin kuwa idan tana tafiya za'a iyajin Qararsu. Sannan kuma indai bata sanya safar Qafa ba, wasu mazajen da ba muharramanta ba zasu iya ganin wannan adon. Yin hakan kuwa haramun ne a Musulunci.
Allah ya umurci matan muminai cewar su boye adonsu kuma kada surika buga kafafunsu yayin da suke tafiya.
(Suratun nuur).
Shi kuwa gyaran gira ta hanyar ragewa gashin ko askewa, Wannan haram ne.
Manzon Allah (saww} ya tsine ma duk matar da take tsigewa gashin girarta da kuma wacce take tsige mata din.
(aduba Sahihul Bukhary hadisi mai lamba 4886 da sahihu muslim hadisimai lamba 2125)
don karin bayani
@ aduba FATAWA AL-LAJNATUD DA'IMAH (juzu'i na 5 shafi na 195-197)
@ Da kuma FATAAWA ULAMA'I BALADIL HARAM shafi na 577.
@ ALFATAWAL HINDIYYA juzu'i na 5 shafi na 357.
@ RADDUL-MUHTAR juzu'i na 6 shafi na 420.
@ MARAQEEL FALAHI shafi na 102.
@ BAHRUR-RAA'IQ juzu'i na 1 shafi na 47

WALLAHU A'ALAM.,

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)