HUKUNCIN MA'AURATA SU JI DAƊI DA BAKINSU DA AL'AURAR JUNANSU (TSOTSAR AL'AURAR JUNA)?


HUKUNCIN MA'AURATA SU JI DAƊI DA BAKINSU DA AL'AURAR JUNANSU (TSOTSAR AL'AURAR JUNA)? 

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamualaikum mal don Allah idon miji na wasa da farjin mace kafin saduwa da sa hannu yana da kyau a musulumci kuma vaya kawu matsala a lapiyar ta.


*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

_Miji shari'a ta bashi dama yaji dadi da matarsa yanda yaso, yaje mata ta inda take haihuwa ta kowanne guri yaso, Kamar yanda Allah yafada acikin aya ta_ _*(223) cikin suratul Baqara.*_
:
_Abu biyu aka haramtawa miji wajan zakkewa matarsa_

      _Nafarko: Saduwa lokacin haila, Kamar yanda Allah yafada acikin ayata_ _*(222) cikin suratul Baqara.*_
:
_Na Biyu: Saduwa ta dubura, Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Tsinanne ne duk wanda yajewa matarsa ta dubura,)_ 
 _*Abu dawda da Ahmad suka ruwaito shi, Albani ya Ingantashi acikin Saheehu jami'i (5889).*_
:
_Duka Ababe biyun Wani hadisin Ya hadesu baki daya, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Ku guji saduwa ta dubura da lokacin Haila)._
_*Ahmad Abu dauda suka ruwaito shi, Yana cikin jami'ussaheeh (1141).*_
:
 _Tsotsar Al'aura da baki, Akwai sharudda guda biyu;_

_*1-* Yakasance hakan baya cutarwa, ko jawo cuta._
_*2-* Kada yazama sababi na wucewar najasa zuwa maqogwaro._

_indai an kiyaye wajen yin yadda baza asha nasaba babu lefi_
.
_Shaik Abdurrahaman yace: Ya kamata Nisantarsa dan Kunya da gujewa Abunda ke tattare dashi na qazanta da Sa6awa fidra da yayi, da lura da cewa zai hana mace biyan buqatarta idan miji ya saba mata dashi._
.
```Wallahu ta'ala a'alam```
:
_*©​​✍🏽 ​​Abdulkadeer Umar Alshinkafawy*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)