HUKUNCIN RUWA BROWN DAKE FITOWA TA GABAN MACE



HUKUNCIN RUWA BROWN DAKE FITOWA TA GABAN MACE 

https://chat.whatsapp.com/BLtOd0SfWGJ9MinvfShFw8

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum
:
Menene hukuncin wani ruwa BROWN dake fitowa ta gaban mace kafin tafara al'ada?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

To shidai wannan nau'i na ruwa BROWN dayake fitowa mata yakasune gida③,
①-kodai yafito kafin haila,
:
②-kokuma yafito bayan mace tagama haila,
:
③-kokuma yafito alokacin da mace take haila,
:
①≈Idan yakasance yafitone kafin haila abinda malamai sukace shine, idan yakasance wannan ruwa kamar wata muqaddimace tazuwan jinin haila to hukuncinsu daya da haila, tayadda ruwan yanazuwa kuma kafin yadauke sai jini yabiyo bayansa, kokuma kafin yafito mace taji wata alama datasaba jinta idan zatayi al'ada, dagabaya kuma saitaga wannan ruwa BROWN yafito to zata dakatar dayin sallah,
:
②≈Amma idan mace taga wannan ruwa batare dataji wata alama nazuwan hailaba, kokuma yakasance ansamu tazara kamar kwanaki ②ko samada hakan tsakanin zuwan ruwan saikuma yadauke to hukuncin tsarkine akanta,
:
③≈Hakanan idan mace taga wannan ruwa yazomata bayan tagama al'ada tayi tsarki to shima bakomai akanta zataci gaba dayin sallah dakuma azumi, saidai akwai malaman dasuke ganin cewa zuwan wannan ruwa kafin jinin haila kokuma yazo bayan angama jini to duk hukuncinsu daya awani QAULIN na Malamai,
:
Ammadai magana mafi inganci itace zuwan wannan ruwan bayan gama jinin al'ada indai ansamu 'yartazara tsakanin daukewar jinin dakuma zuwan ruwan to wannan baya hana mace tacigaba dayin ibadarta,
:
Amma idan yakasance mace taga wannan ruwane atsakanin al'adarta kamar ace tayi kwana ② jini yana zuwa mata akwana na③ kuma saitaga wannan ruwa yafito sannan akwana na④ ko na⑤ saitasake ganin jini, to wannan ruwa hukuncinsa daya da jinin al'ada mace zata jirane harsai yadauke sannan tayi wanka,
:
Mai neman karin bayani sai yaduba wadannan litattafai kamar haka:
: ↓↓↓
:
ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ ﺍﻟﻄﺒﻴﻌﻴﺔ ﻟﻠﻨﺴﺎﺀ ‏( ﺹ 19 ‏)
:
ﺛﻤﺮﺍﺕ ﺍﻟﺘﺪﻭﻳﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ‏( ﺹ 25 ‏)
:
ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ‏( 18/296 ‏)
:
ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ‏( 1/202 ‏)
:
ﺍﻟﻤﺠﻤﻮﻉ ‏( 2/422 ‏)

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)