HUKUNCIN YIN SALLAH DA TUFAFI MAI HOTO
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
*TAMBAYA*❓
Assalam Don Allah MALAM riga mai hoton mutum ,za a iya sallah da ita?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Bai haltta sanya tufar datake da hoton mutum ko dabba ba, saboda hadisin da *Bukhari ( 3226) da Muslim ( 2106) Suka ruwaito* Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Mala'iku basa shiga gida ko dakinda yakeda hoton abu mai rai)
*Duba Madalibul Ulil Nahayi ( 1/353)*
An tambayi shaik Usaimeen *Menene hukuncin Sanya tufafin dasuke da hoton mutum ajikinsu ko dabbobi?*
Ya Amsa dacewa: Bai halatta ga Mutum yasanya tufafinda yake dauke da hoton mutum ko dabba ba, haka kuma bai halatta yasanya hula ko mayafi ko safa ko abunda yaikama da haka wanda yakeda hoton mutum ko dabba ajikinsa, saboda ya tabbata daga Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Mala'iku basa shiga gida ko dakinda dayake akwai hoto acikinsa) Hoton Abango aka likashi ko yana ajiye acikin album na ajiye hotuna, ko sauran gurare, saboda haka muke ganin haramcin yin hoto wai saboda tarihi ko tunawa da mutum, kamar yanda wasu suke fada, domin zaman wadannan hotuna yana hukuntar da haramcin shiga gida ko daki ga mala'iku.
Yasake cewa: Malamai sunce haramunne sanyawa karamin yaro tufafi masu hotunan mutum ko dabbobi, kamar yanda yake haramun ga babba, Abunda yakamata ga musulmi shine ya kyakketa irin wadannan kayan datakalman, dan kada mabarnata su shigo mana tawadannan hanyoyi, amma idan aka yanke aka toshe wannan kofar bazasu samu kofar dazasu shigar dasu zuwa garuruwan musulmai ba, damaida al'amarin yazama sassauka, *fatawa shaik Usaimeen ( 12/333).*
Abu na biyu: *Menene ingancin Sallar wanda yayita datufafinda yake da hoton mutum ko dabbobi*
Wanda yai Sallah datufafinda yake akwai hoton mutum ko dabba ajikinsa sallarsa tayi tareda zunubin sanya riga mai hoton dayayi,
An Tambayi Malaman majalisar ilimi dafatawa nakasar Saudiyyh *shin yahalatta yin sallah datufa mai hoton mutum ko dabba, kuma ya halatta shiga bandaki datufafin dayake dasunan Allah ajikinsa,?*
Sai Suka Amsa: Bai halatta yin sallah da tufafinda yake da hoton abu mai rai ajikinsaba, hoton mutum ne kona dabbobi, kona tsun-tsaye ko duk abunda yake darai, haka bai halatta sanya tufafinba koda ba sallah mutum zaiyiba, sallar wanda yayita datufafi mai hoton abu mairai tayi tareda zunubin sanyata gawanda yasan hukuncin shari'a akan hakan, amma yayi sallar da ita, Bai halatta rubuta Sunan Allah ajikin tufafi ba, bai halatta shiga bandaki da tufafinda yake akwai sunan Allah ajikiba, sai idan bukatace takama ta dole, saboda Abindake cikin hakan na wulaqanta sunan Allah.
*fatawa laj-natul da'imah ( 6/179)*
Shaik Usaimeen rahimahullahu yace: Wanda yai sallah datufafi mai hoton Abu mairai idan ya jahilci hukuncin sanya tufafi mai hoto ko hukuncin sallah dashi, sallarsa tayi tareda zunubin sanya tufafin abisa zance mafi inganci cikin zantukan malamai, daka cikin malamai akwai wadanda sukace: *sallarsa tabaci saboda yayi sallah da tufafinda yake haramun agareshi*
*Fatawa Shaik Usaimeen ( 12/360)*
Abisa wannan wajibine cire hotunan alfadarai ko kada ko mage dasauransu daka jikin tufafi ko dena sanyasu, ko shafe hoton dafenti ko rinashi da abunda zai gusar da alamar hoton, ko sanya wani abun kadinke wajan dadai sauran abunda zai rufe hoton koya boyeshi baza'a ganshi ba, in mutum yai sallah datufafin dasauran alamun hoton ajikin tufar sallarsa tayi amma tareda zunubin sanyata akansa.
Wallahu A'alamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﻧﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﻧﺘﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*