HUKUNCIN SALLAR MACEN DA BATA RUFE KAFAFUN TA BA
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum malam ina hukuncin sallar mace kafanta a waje?.
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Hukuncin sallar wacce bata rufe ƙafafunta ba, mas'ala ce wacce Malamai suka yi saɓani a kai, inda wasu ke ganin cewa sallar ta bata inganta ba, kamar Malikiyya da Hanabila, duba da hadisin Ummu Salma da yace
عن أم سلمة رضي الله عنها أنها سألت النبي صلى الله عليه وسلم : أتصلي المرأة في درع وخمار ليس عليها إزار ؟ قال : ( إِذَا كَانَ الدِّرْعُ سَابِغًا يُغَطِّي ظُهُورَ قَدَمَيْهَا ) .
Wannan ita ce fatawar Bn Baaz da Shafi'iyya.
Amma Hanafiyyah na ganin sallar ta, ta inganta, duba da cewa ƙafar mace ba al'aura bace. Wannan ita ce fatawar Shaikh Uthaymin kuma shine abin da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya tafi a kai. Don ba a ruwaito matan Sahabbai na saka huffi ko safi kafin suyi sallah ba, sannan ko da mace ta rufe ƙafafunta, idan ta yi sujuda, za su baiyana. Wannan zance kuwa shine mafi rinjaye da inganci a wuri na.
Amma don mace ta fita daga saɓanin Mallamai, zai fi kyau da kamala ta saka safa ko ta rufe ƙafafunta idan za tayi sallah.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*