HUKUNCIN SANYA EYELASHES

HUKUNCIN SANYA EYELASHES

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum warahmatullah.

 Malam mene hukuncin saka eyelashes da 'yan mata suke yi ko amare a lokacin biki in an gama biki su cire, wasu sukan cire a ranar wasu kuma suna barin sa ya yi kwanaki, ya hukuncin alwala, saboda da gum ake sa shi kuma ina kyautata zaton ruwa ba ya taba wurin, shin sanyawar kansa ba matsala, ko kuma idan za a cire lokacin da za a yi alwala za a iya sakawa? Nagode.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salámu Wa Rahmatullahi Wa Barakátuhu. 

Ga 'yan uwana maza da ba su san ko mene ne eyelashes ba shi ne qirqirarren gashin ido da mata suke qarawa a lokacin bukukuwa da manufar nuna ado.
Kafin in ba da amsar tambayar nan, na tuntuɓi mata a Zaurukan Saqon Annabta sashen mata zalla da kuma wajen zauren a game da matsayin eyelashes, shin ruwan alwala yana tsuma gam (gum) ɗin da ake manne gashin da shi har ya kai ga fatar ido ko ba ya tsuma shi? Mafi yawan su sun tabbatar min da cewa ruwa ba ya ratsa gam ɗin da ake amfani da shi har ya iske fatar ido, ga biyu daga cikin amsoshin da suka ba ni:

"Assalamu alaikum malam barka da qoqari. A gaskiya ruwa ba ya taɓa fatar matar da ta sa eyelashes. Kuma shi ma tamkar canza halittar Allah ne, don da zarar an sanya shi sai mace ta canja. Wallahu A'alam."

"Assalamu Alaikum, malam barka da warhaka, to a gaskiya ruwa ba zai taɓa ratsa wurin da aka Sanya Shi ba. Saboda gum ne ake Sanya shi a jikin gashin idon da za a kara, to ka ga duk inda aka manna to fa zai lulluɓe wurin ne, ka ga ruwa ba zai ratsa shi ba, duba da idan ka zuba gum a wurin idan ka zuba ruwa a wurin ba zai ratsa gum din ya sauka karkashin sa ba, ka ga faruwar haka zai haifar da lam'a a cikin alola, Allah ya kara wa malam lafiya."
A bisa lura da amsoshin nan nasu, duk da cewa akwai masu amsa akasin nasu, sai ya zama bai halasta mace ta yi alwala da eyelashes har ta yi sallah da shi idan har ya tabbata da gaske ruwa ba ya tsuma gam ɗin da ake manne shi da shi har ya kai ga fatar ido ba, saboda in hakan ya tabbata, to zai sa a sami lum'a a fatar ido a lokacin alwala.
Idan aka faɗaɗa ma'anar hadisin haramcin qarin gashi, to za a iya cewa la'anar da Manzon Allah ﷺ ya yi a kan mai qarin gashi da wadda ta nemi a qara mata a hadisin Muslim (2122), wannan la'ana ta haɗa da har mai qara gashi a ido, wato eyelashes, saboda duk cikin su qarin gashi ne a bisa gashin asali.
Duba Amsoshin Tambayoyin ku na 039 don ganin maganganun malaman Musulunci a kan rabe-raben hukuncin qarin gashi.
Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF**HUKUNCIN SANYA EYELASHES* 

 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)