HUKUNCIN WANDA BAYA WASA DA GABANSA, AMMA IN SHA'AWA TA DEBE SHI YANAYI DA PILLOW
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum To malam inada tambaya shi wanda ba wasa yakeyi da alaurarsa ba amma idan yaji shaawa to xai kwanta katifa yakama yi kamar yana saduwa da mace sai ya kawo to minene hukuncin wanan malam
Sannan kuma idan mutum ya kalli fina finan batsa ya kawo to wanan istimnai ne
*AMSA*👇
Wa,alaikumussalam eh duka sun shiga cikin haramcin domiN ALLAH ya haramta yin hakan, yakuma kira duk masu aikata irin haka da Qetare iyaka.
Sannan manzon ALLAH yayi kira ga matasa da suyi Aure in sunada hali in babu suyi azumi dan zai zama musu kariya.
Amma fa auren shine dai dai dan azumin kadan yake ragewa.
Idan kuma ka futar da maniyii wanka ya kamaka dole.
Da wannan muke kira dan ALLAH a taimaka a samari da 'yan mata suyi ma yayan su Aure, idan fa suka lalace dukkan ku kunada laipi domin baku kula dasu ba.
ALLAH cewa yayi "ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta..."
Kar kaidan kayi Aure dan ka yakai shekara 23 ko sama da haka ko qasa da haka yace ma yanason Aure kai kuma kacemar saiyayi makaranta.
Ana samun matsala wai sai ace ai namijine kai, to idan ba'a barka kayi Auren ba ita maen wa zai Aure ta??
Dan ALLAH Kuji tsoron ALLAH ku taimaka a yaranku suyo Aure kar kuma kuyi musu Auren dole dan haramun ne.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::
_Dan uwanku a musulunci._
*MUHAMMAD AUWAL ABU JA'AFAR AL-POTISKUMAWI*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*