KARATUN ALQUR'ANI DA KALLON MUS'HAFI



KARATUN ALQUR'ANI DA KALLON MUS'HAFI

Sahabi Abdullah bin Mas'ud Allah ya ƙara masa yarda yana cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce "Duk wanda yake son ya so Allah da Manzonsa to ya karanta Alqur'ani yana mai kallon mus'hafi".
السلسلة الصحيحة ٢٣٤٢

Sahabi Ibnu Mas'ud Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; "ku yawaita kallon mus'hafi"
المصنف لابن أبي شيبة ٢/٤٩٩

Imam An-Nawawi Allah ya masa rahama yana cewa; "Karatun Alkur'ani da kallo shi ya fi falala akan karanta shi da ka, domin kallon mus'hafi din shima ibada ne da ake son mutum ya aikata, dan haka karantawa da kallo zai zama ibada ne guda biyu a haɗe (ibadar kallo da ibadar karatun)".
التبيان في آداب حملة القرآن ٥٥

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)