KU KASHE FITILU YAYIN KWANCIYA BACCI DON KAUCEWA GOBARA



KU KASHE FITILU YAYIN KWANCIYA BACCI DON KAUCEWA GOBARA

Haƙiƙa Barin Kowace Irin Wuta a Kunne Yayin Kwanciya Bacci Hanyace Daga Cikin Hanyoyin dake Haifar da Gobara a Gida Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عَنْ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ *(احْتَرَقَ بَيْتٌ بِالْمَدِينَةِ عَلَى أَهْلِهِ مِنْ اللَّيْلِ فَحُدِّثَ بِشَأْنِهِمْ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ إِنَّ هَذِهِ النَّارَ إِنَّمَا هِيَ عَدُوٌّ لَكُمْ فَإِذَا نِمْتُمْ فَأَطْفِئُوهَا عَنْكُم)
 {رواه البخاري}

An Kar6o Daga Abi-Musa (ra) Yace: Wani Gida Ya Ƙone Da Daddare a Garin Madina, Sai Manzon Allah (ﷺ) Ya Bada Labarin Dalilin Halin da Suka Tsinci Kansu a Ciki; Yace: “Lallai Wannan Wutar Maƙiyarku Ce, Idan Zakuyi Bacci, To Ku Kasheta”.
(Bukhari) 

A Wani Hadisin Kuma Manzon Allah (ﷺ) Cewa Yayi:

عَنْ سَالِمٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ :(لا تَتْركوا النَّارَ فِي بُيُوتِكُمْ حِينَ تَنَامُون)
(متفق عليه)

An Kar6o Daga Salim, Daga Mahaifinsa, Daga Annabi (ﷺ) Yace: “Kada Kubar Wuta a Cikin Gidajenku a Yayin da Zakuyi Bacci”.

(Bukhari da Muslim)

ALLAH UBANGIJI YA TSARE MANA RAYUKAN MU DA DUKIYOYIN MU DAGA FITINAR GOBARA

ZAKU IYA BIBIYAR MU TA WAƊANNAN HANYOYIN SADARWAR👇🏽👇🏽

WHATSAPP
 +2347055883010

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

TELEGRAM:
https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg
Post a Comment (0)