HUKUNCIN WANI FARIN RUWA KO KUMA WANI DANSHI DAKE FITA DAGA GABAN MACE



HUKUNCIN WANI FARIN RUWA KO KUMA WANI DANSHI DAKE FITA DAGA GABAN MACE.

https://chat.whatsapp.com/BLtOd0SfWGJ9MinvfShFw8


*TAMBAYA*❓

Salamun alaikum
Malam menene hukuncin wani farin ruwan kokuma danshin dayake fitowa mace ta gabanta, idan ta ganshi a pant dinta lokacin daxatayi
Sallah dolene saita cire pant din kokuma zata iyayin Sallah dashi?


*AMSA*👇

Wa alaikumussalam
Dangane da magana akan farin ruwan dakan fito daga farjin mace malamai sunyi sabani akansa,
Magana tafarko itace Malaman Mazhabin
SHAFI'IYYA dakuma HANABILA, Suntafine
akancewa ruwan dake fitowa daga farjin mai
tsarkine danhaka koda yataba tufafi to za'a
iyayin sallah dashi ahaka basai anwankeba sukace babu dalilin daya nuna cewa wannan ruwan ba mai tsarki bane kuma a ASALI komai mai tsarkine sai in ansami dalilin dayazo yace ba mai tsarki bane,
Magana tabiyu kuma itace QAULIN da Malaman Mazhabin MALIKIYYA dana HANAFIYYA Sukatafi akansa cewa ruwan dake fita daga farjin mace najasane danhaka idan yataba tufafi to dole sai anwankeshi sannan ayi sallah dashi, to maganar datafi INGANCI itace wannan ruwa kokuma
danshin dake fita daga farjin mace ba najasa
bane, saboda ba'asamu wani DALILI dayanuna cewa najasa ne,
Sannan kuma Malamai sunsakeyin wani sabanin akancewa shin fitar wannan ruwan yana warware alwala ko baya warwareta? Mafi rinjayen malamai
sukace fitarsa yana warware alwala, domin
sunaganin cewa ruwan dakefita daga farjin mace hukuncinsa daidai yake da hukuncin mace mai
jinin ISTAHADHA, shiyasa suka kafa hujja dacewa Manzon Allah (SAW) Ya umarci mai jinin
ISTAHADHA dacewa tarikayin alwala akowacce Sallah, danhaka sukace shima wannan DANSHIN ko ruwan dakefita daga farji za'a riskar da
hukuncinsane da na mai ISTAHADHA,
Amma akwai malaman dasuke ganin cewa fitar wannan ruwa baya warware alwala kamar yadda
( ﺇﺑﻦ ﺣﺰﻡ ﺍﻟﻈﺎﻫﺮﻱ )
Yakawo acikin littafinsa maisuna:
ﺍﻟﻤﺤﻠﻲ ﺑﺎﻵﺛﺎﺭ
To saidai Malamai sukace wannan maganar tasa bashida wani ingantaccen dalili akanta,
Danhaka Magana mafi inganci acikin zantukan da malamai sukayi akan wannan matsala itace cewa ruwan dake fitowa daga farjin mace idan
yakasance yafitone daga cikin mahaifa to ruwane mai tsarki danhaka koda yataba tufafi ko Pant to za'a iyayin Sallah dashi batare da an wankeba,
amma idan wannan ruwa yafitone daga kofarda fitsari yake fitowa to najasane, sannan kuma idan mace tanada alwala saitaga wannan ruwan
yafitomata to alwalarta ta warware danhaka dole sai tasake wata.
*Mai neman karin bayani sai yadubaw wadannan litattafai kamar haka*
ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ } 1/332 {
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ } 21/221 {
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ } 1/284 }
_ Dan uwanku a muslunci._
_*MUSTAFA U.S ASSALAFY.*_

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)